No menu items!

Sample Page Title

Date:

An kama wani da ya saci akuya a barikin ’yan sanda

Wani mai suna Chukwudi Ugwu ya gurfana a gaban wata kotun majistare a Ibadan Jihar Oyo bisa zarginsa da satar akuya a wani barikin yan sanda.

Mai gabatar da kara DSP Adewale Amos ya shaida wa kotun cewa wanda ake ƙara da wasu da suka gudu sun shiga Barikin ’Yan sanda na Iyaganku, Ibadan suka sace akuyar da kuɗinta ya kai naira dubu 250 mallakar Olawole Oke.

KU KUMA KARANTA: Ƴan sandan Najeriya sun kama waɗanda ake zargi da satar mutane a titin Abuja-Kaduna

Kuma ya zarge su da sace babur ƙirar Bajaj da ta kai Naira dubu 250 ta wani mai suna Dabid Adepoju, wanda hakan ya saba wa sassa na 516 da 390 (9) na dokokin manyan laifuffuka na Jihar Oyo.

Alkalin Kotun, Maruff Mudashiru ya ba da belin wanda ake zargin a kan Naira dubu 200 tare da dage shari’ar zuwa ranar 11 ga Yuli mai zuwa.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...