Sojoji sun ceto mata da yara 386 daga dajin Sambisa

0
69

Sojoji sun ceto mata da yara 386 daga dajin Sambisa

Aƙalla mutane 386 ne akasari mata da ƙananan yara ne Sojojin suka ceto daga dajin Sambisa shekaru goma bayan sace su.

Muƙaddashin rundunar ta GOC 7, AGL Birgediya Janar  Haruna ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a wajen dajin Sambisa a ƙaramar hukumar Konduga bayan ya karbi baƙuncin sojojin da suka gudanar da aikin na kwanaki 10.

Birgediya Janar Haruna, ya ce farmakin da aka yi wa laƙabi da “Operation Desert Sanity 111” an yi shi ne domin tsarkake dajin Sambisa daga dukkan ragowar ‘yan ta’addan tare da samar da wasu daga cikin su masu kwadayin mika wuya kamar yadda aka samu damar yin hakan.

KU KUMA KARANTA: An ceto ɗaliban jami’ar Jihar Kogi da aka sace

“Mun kuma ceto wasu fararen hula; Ya zuwa jiya mun ceto 386 kuma na tabbata adadin zai karu zuwa wani lokaci  inji Birgediya Janar Haruna.

 Birgediya Janar Haruna  ya yi wa sojojin jawabi kan sakon babban hafsan sojin Najeriya da kuma  yabawa da kwazon da suka nuna a lokacin aikin, ya kuma bukace su da su ci gaba da gudanar da aikin. Wasu daga cikin wadanda aka ceto daga dajin Sambisa da suka yi magana, sun ce sun shafe shekaru 10 a hannun su.

Leave a Reply