Nan da mako huɗu Najeriya za ta daina sayo man fetur daga waje — Ɗangote

0
51

Nan da mako huɗu Najeriya za ta daina sayo man fetur daga waje — Ɗangote

Nan da shekara uku zuwa huɗu nahiyar Afirka ba za ta sake sayen takin zamani daga waje ba.

Matatar man Dangote da ke Jihar Legas ta ce Najeriya za ta daina sayo man fetur daga waje a watan Yuni, a ƙoƙarin da ƙasar ke yi na samun dogaro da kai a fannin makamashi.

Mai matatar, Alhaji Aliko Ɗangote shi ne ya bayyana haka a taron kolin shugabannin kamfanoni na Afirka ranar Juma’a a Kigali, babban birnin Rwanda.

Hamshakin attajirin ya ce, matatar za ta samar da man da ake bukata a cikin gida ba ga Najeriya ba kadai har ma da sauran kasashen yankin Afirka ta yamma.

KU KUMA KARANTA: Ɗalibi ya lashe N5 miliyan a tallan siminti na Dangote

Ɗangote ya ce, a cikin watan Yuni, wato nan da mako huɗu zuwa biyar, ba wani mai da Najeriya za ta rika saye daga waje.

“A yanzu Najeriya ba ta buƙatar shigo da wani man fetur kuma zuwa wani lokaci a watan Yuni, nan da makonni huɗu ko biyar masu zuwa, bai kamata Najeriya ta ƙara shigo da wani abu mai suna man fetur ba, ko da kuwa ɗigon lita ɗaya ne.

“Muna da isasshen man fetur da dizel da za mu ba aƙalla Afirka ta Yamma da Afirka ta Tsakiya.

“Muna da isasshen man jirgin da za mu ba duk nahiyar Afirka da kuma fitar da shi zuwa Brazil da Mexico.

Ya kara da cewa: “Matatar mu tana da girma sosai, kuma wannan abu ne da muka yi imani cewa Afirka na buƙata.

“Abin takaici idan aka dubi nahiyar Afirka baki ɗaya, ƙasashe biyu ne kawai ba sa shigo da man fetur — daga Aljeriya sai Libya kawai — amma ragowar duk suna shigo da shi ne.

“Don haka, ya kamata mu sauya wannan tsari mu tabbatar da cewa ba wai kawai mu je muna haƙo ɗanyen man fetur ba, ya kamata mu riƙa tace wanda zai wadatar da mu a nan cikin gida kuma a samar da ayyukan yi.”

Bayan man fetur, Dangote ya ce matatar za ta kuma samar da isasshen man dizil ga Afirka ta yamma da ma Afirka ta tsakiya.

Haka kuma ya ce, matatar za ta iya samar da isasshen man jirgin sama ga nahiyar Afirka gaba daya, har ma ta fitar da shi zuwa kasashen Brazil da Mexico.

Attajirin wanda ya fi kowa kudi a Afirka ya kuma bayyana cewa, nan da shekara uku zuwa huɗu nahiyar Afirka ba za ta sake sayen takin zamani daga waje ba, domin matatar za ta wadata nahiyar da takin.

Matatar man ta Dangote bayan soma aiki a watannin bayan nan na iya tace gangar ɗanyen mai 650,000 duk rana, kuma idan ta fara aiki ɗari bisa ɗari za ta zama mafi girma a Afirka da Turai.

Leave a Reply