No menu items!

Sample Page Title

Date:

Marasa biyan kuɗin lantarki ne ke ƙorafin ƙarin ƙuɗi – Minista

Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce kukan da ake yi kan karin kuɗin wutar lantarki ga masu amfani da layin Band A ya fito ne daga wadanda ba sa biyan kudin wutar a baya.

Adelabu, ya bayyana hakan a taron da aka yi kan Kasuwar Makamashi na Afirka karo na 8 a ranar Alhamis a Abuja.
Ya ce sabon tsarin farashin makamashi ya haifar da rage farashin lantarki ga masu amfani da rukunin Band A da kashi 30 zuwa 40 cikin ɗari.

Ministan ya yi zargin cewa, sabon kudin fiton ya sa aka kara kudin da ake samarwa ga masana’antun, wanda hakan ya janyo tsadar kayayyaki da ayyuka.

“Ƙarin kuɗin wutar lantarkin ba wai an yi niyyar ne haka kawai ga ’yan Najeriya ba, ko kuma ƙara tabarbarewar tattalin arzikin kasa da ya riga ya yi sanadin hauhawar farashin kayayyaki da rage darajar Naira.

KU KUMA KARANTA: Majalisa ta amince wa Tinubu ciyo bashin $500m don sayen mitocin lantarki

“Amma an yi niyya ne don magance ko rage wahalhalun da jama’a ke ciki.

“Waɗanda ke rukunin A, idan za su kwatanta abin da suke kashewa wajen samar da makamashi daga wutar lantarki da na’urorin samar da makamashi, kafin sake sauya kuɗin fito, ba su samu kasa da kashi 30 zuwa 40 ba, a jimillar kuɗin su. Wannan ita ce gaskiya.”

“Mu ma masu amfani da wutar lantarki ne, don haka za mu iya tabbatar da hakan.

“Gaskiya ne cewa idan kuna cikin tsarin Band A, lissafinku zai ninka idan ba ƙari ba.

“Amma duba abin da kuke kashewa a kan janareta da sayen dizal da sayen man fetur, sabon tarin bai kai haka ba,” in ji ministan.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...