Babbar Kotun MƊD ta fara sauraron ƙara kan afka wa Rafah da Isra’ila ta yi

0
58

Babbar Kotun MƊD ta fara sauraron ƙara kan afka wa Rafah da Isra’ila ta yi

Babbar Kotun Majalisar Ɗinkin Duniya ta fara sauraron ƙara ta kwanaki biyu game da buƙatar Afirka ta Kudu ta neman kotun ta umarci Isra’ila da ta dakatar da hare-haren soji kan garin Rafah na Kudancin Gaza.

A karo na huɗu, Afirka ta Kudu ta bukaci kotun kasa da kasa kan matakan gaggawa tun bayan da kasar ta shigar da karar farko tana zargin Isra’ila da ikata kisan kiyashi a Gaza.

Bukatar baya-bayan nan ta bayyana cewar roƙon da aka yi na farko da matakin da Hague ta dauka bai isar ba wajen magance “Munanan hare-haren soji kan ‘yan gudun hijirar Gaza.”

Isra’ila ta bayyana Rafah a matsayin yankin ‘yan gwagwarmayar Falasɗinawa na Hamas, suna watsi da gargaɗin su kauce wa gargadin Amurka kan nisantar duk wani abu da zai illata fararen hula.

KU KUMA KARANTA: Sojojin Isra’ila sun kama Falasɗinawa 28 a Gabar Yamma da Kogin Jordan

Afirka ta Kudu ta buƙaci kotun da ta umarci Isra’ila ta janye daga Rafah; ta dauki matakan tabbatar da jami’an MƊD, ma’aitan jinƙai da ‘jaridu sun shiga yankin Gaza, sannan ta ba su rahoto cikin mako guda kan yadda take aiki da wannan buƙata.

A watan Janairu, Alkalai sun umarci Isra’ila da ta nisanci kisa, rushe gine-gine da duk wani nau’i na kisan kiyashi a Gaza, amma tawagar alkalan sun dagakar da bayar da umarnin a daina kai hare-haren da suka mayyar da yankunan Falasɗinawa kamar bola.

A umarni na biyu a watan Maris, kotun ta ce dole ne Isra’ila ta dauki matakan inganta ayyukan jinƙai a Gaza, ciki har da bude karin hanyoyin kai kayan abinci, ruwa, man fetur da sauran kayayyaki.

Mafi yawan jama’ar Gaza su miliyan 2.3 sun rasa matsugunansu tun bayan fara kai hare-haren Isra’ila.

Afirka ta Kudu ce ta fara kai karar a watan Disamban 2023 kuma tana kallon matakin shari’ar ya samo asali ne daga yadda ƙasar take.

Jam’iyya mai mulki a Afirka ta Kudu ta ANC, ta sha kwatanta ta’annatin da Isra’ila ke yi a Gaza da da Jammacin Gabar Kogin Jordan da abinda kasarsu ta fuskanta a tarihi na gwamnatin farar fata tsiraru, wanda ya hana mafi yawan baƙaƙen fata katabus, mulkin nuna wariyar ya zo ƙarshe a 1994.

Leave a Reply