Rundunar sojin Najeriya ta nemi Nijar ta kama shugaban ‘yan bindiga da take nema

0
49

Rundunar sojin Najeriya ta nemi Nijar ta kama shugaban ‘yan bindiga da take nema

Rundunar sojin Najeriya ta nemi maƙwabciyarta Nijar da ta kama wani shugaban ‘yan bindiga da ta ce tana nema ruwa a jallo a ƙasar, kamar yadda mai magana da yawun hedkwatar tsaro ya faɗa a ranar Alhamis.

Mai magana da yawun Hedkwatar Tsaron Edward Buba ya ce Halilu Buzu ɗan ƙasar Nijar kuma shi ne babban mai samar da makamaki a Najeriya daga masu sayar da su a Libiya.

A wata sanarwa, Buba ya ce Buzu yana kuma aiki a wani wajen haƙar zinare a Zamfara, ɗaya daga cikin jihohin da ke fama da matsalar satar mutane.

“A lokacin da dakaru suka kusa cim masa, sai ya tsallaka kan iyakar Jamhuriyar Nijar don neman mafaka,” in ji Buba.

KU KUMA KARANTA: ’Yan bindiga sun sace ɗalibai a Jami’ar Jihar Kogi

“A wannan lokacin, muna bi ta hanyoyin da suka dace dona kira ga hukumomin Nijar da su kama shi, tare da hukunta shi kan wannan ta’asa da ya aikata.”

A watan Nuwamban 2022, sojojin Najeriya sun ce sun kashe Halilu Buzu tare da wasu shugabannin ƙungiyoyin masu garkuwa da mutane, amma Buba ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a ranar Alhamis cewa “ba sabon abu ba ne a ce mutane daban-daban suna da suna iri ɗaya ko da a tsakanin ‘yan ta’adda.”

Rundunar sojin ta ce ‘yan bindigar da ke da alaƙa da ƙungiyar Buzu sun kashe mutum 19 a wani ƙauye a makon da ya gabata a wani hari da suka kai a Zamfara.

Yankin arewa maso yammacin Najeriya ya shafe shekaru yana fama da matsalar ‘yan fashi, lamarin da ya yi sanadin kashe dubban mutane.

Leave a Reply