Tinubu ya karɓi baƙuncin shugaban Senegal, Bassirou Faye

0
112

Tinubu ya karɓi baƙuncin shugaban Senegal, Bassirou Faye

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya karɓi baƙuncin Shugaban Senegal, Bassirou Diomaye Faye a fadar Aso Rock da ke Abuja.

Wannan shi karo na farko da shugaban mafi ƙarancin shekaru a nahiyyar Afirka ya kawo ziyara Najeriya tun bayan zamansa Shugaban Senegal a watan Afrilun da ya gabata.

Bayanai sun ce Bassirou Diomaye Faye mai shekaru 44 ya zo ziyarar aiki ne a Najeriya.

Sai dai zuwa babu masaniya a kan aikin da ya kawo Shugaban Senegal ɗin Najeriya.

A watan Afrilu da ya gabata ne aka rantsar Bassirou Diomaye Faye a matsayin shugaban Senegal.

KU KUMA KARANTA: Majalisa ta amince wa Tinubu ciyo bashin $500m don sayen mitocin lantarki

An rantsar da ɗan jam’iyyar adawar bayan ya ni nasara da kashi 54 cikin ɗari na kuri’un da aka kaɗa a zaɓen a kan abokin hamayyarsa na hadakar jam’iyyu masu mulki.

Tinubu, wanda shi ne shugaban ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen yammacin Afirka (ECOWAS), ya karɓi bakuncin Bassirou Faye tare da wasu ƙusoshin gwamnatin ƙasar.

Leave a Reply