Wani tsoho da shekara 71 zai yi zaman kaso na tsawon shekaru biyu sakamakon kama shi da hodar ibilis a Kano.
Lauya mai kare tsohon ya ce wannan ne karo na farko da tsohon ya yi aniyar amfani da hodar iblis kuma ya yi nadama.
Sai dai lauya mai gabatar da kara, Aminu Muhammad, yayin gabatar da hujjoji ya tunatar da kotun cewa hodar iblis ba kamar tabar wiwi ba ce, don haka ya kamata a yanke masa hukunci mai tsanani.
Mai shari’a Muhammad Nasir Yunusa na babbar kotun tarayya da ke jihar Kano, ya yanke wa tsohon tijon mai suna Okey Okosa dan shekara 61 da haihuwa hukunci zaman gidan yari na shekara biyu.
KU KUMA KARANTA: Ana zargin ‘ma’auratan bogi’ da ɓoye hodar-ibilis a al’aura
An dai kama tsohon ne da laifin mallakar hodar ibilis da ta kai kimanin nauyin gram 2.3.
Wannan ya saba wa sashe na 20 (1) da (c) na dokar kasa da ta tilasta bin doka da oda ta NDLEA.
Okasa ya amsa laifinsa, ya kuma bayyana cewa ya yi nadama.