Shugaban NILEST ya baiwa gwamnatin Najeriya shawara kan yadda za a farfaɗo da masana’antu a ƙasa baki ɗaya

Daga Idris Umar, Zariya

Babban Darakta kuma shugaban Cibiyar kimiyyar Fata ta Najeriya (NILEST) dake Samaru Zariya, Farfesa Yakubu ya yi ƙira ga masu ruwa da tsaki, tare da masu bincike, musamman masana’antu, masu saka hannun jari, a ma’aikatun gwamnati da saura cibiyoyi masu zaman kansu da ke Zariya da su zo don samar da wata hanya ta haɗin guiwa da za a samu ci gaba a masana’antun dake faɗin jihar Kaduna musamman ƙasar Zazzau a halin yanzu.

Babban daraktan ya bayyana hakan ne a jawabinsa na ƙarƙare taron kasuwanci da saka hannun jari na ƙasa da (ZANETIS) ta shirya a ranar Asabar a filin Polo dake GRA Zariya ƙaramar hukumar Sabon Gari.

Farfesan ya ƙara da cewa, taron an shirya shi ne domin baje kolin zuba hannun jari a harkar noma da ayyukan haɗin guiwa a kimiyanci don samun fahimta lamarin cikin sauƙi.

Shugaban ya tabbatar da cewa lokaci ya wuce na dogara da satifiket kaɗai a ɓangaren neman abinci.

Kuma ya nuna cewa wannan taron ya na ƙira ne ga dukkan al’umma da su fito don tarbar nazarce-nazarce, don bunƙasa kaifin basirarsu da Allah ya basu kuma su kasance cikin shirin yin gogayya da sauran ƙasashen duniya wajan amfani da ilimin kimiya.

KU KUMA KARANTA: Hamas ta amince da shawarar Qatar da Masar ta tsagaita wuta a Gaza na — Haniya

Shugaban ya yi tambaya kamar haka, Shin wanene ya mallaki biranenmu da suka yi fice ta fuskacin kasuwanci a halin yanzu?

Kuma ya amsa kamar haka “Tabbas, ba waɗanda suka fi kowa yawan satifiket ɗin karatu bane”

Yace ɗaya daga cikin manufofin wannan taron shi ne gwama karatu da kuma ƙwarewa, bincike tare da bunƙasa kasuwanci da aiki tuƙuru don kawo ci gaban ƙasa.

Mai Martaba Sarkin Zazzau Dakta Ahmed Nuhu Bamalli wanda Hakimin ƙasar Gubuchi, Alhaji Dakta Bello Lawal ya wakilce shi tuni Hakimin ya yi alƙawarin bai wa taron duk wata haɗin kai da suke da buƙata wajen ganin manufarsu ya kai gacci.

Masana’antu da manyan cibiyoyi da dama ne dake Zariya da kewaye suka halarci taron na kwanaki goma.

Kuma tabbas kamfanoni masu ƙaramin ƙarfi sun yabawa wanda suka shirya taron.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *