Mutum 12 sun mutu a rikicin da ya biyo bayan zaɓen shugaban ƙasa a Chadi

0
99

Aƙalla mutane 90 aka samu tabbacin sun ji raunuka iri-iri a N’djamena, babban birnin ƙasar.

Hukumomi Chadi sun tura dakaru sassan ƙasar don su kwantar da tarzomar da ta ɓarke bayan zaɓen shugaban ƙasar da aka yi, inda alƙaluma ke nuna cewa adadin mutanen da suka mutu a ranar Asabar ya kai 12 a lokacin haɗa wannan rahoto.

Gidan talbijin na Chadi ya ba da rahoton cewa an haramta ajiye makamai ko yin amfani da su a ƙasar wacce ke tsakiyar nahiyar Afirka.

KU KUMA KARANTA:An ji harbe-harben bindiga a birnin N’djamena na Chadi

Rahoton ya ce an haramta makaman ne bayan da aka samu asarar rayuka tara a daren Alhamis bayan da aka sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasar da aka yi a ranar 6 ga watan Mayu.

‘Yan sandan Chadi sun ce wasu mutane uku da suka ji rauni sun mutu a asibiti a N’djamena a daren Juma’a yayin da wasu fararen hula 30 suka ji rauni a wani faɗa da ya ɓarke.

Shugaban mulki soja, Mahamat Deby ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasar sai dai abokin hamayyarsa Succes Masra na ƙalubalantar sakamakon.

Leave a Reply