Gwamna Raɗɗa ya biya kuɗin Hadaya ga dukkanin alhazan Katsina

0
101

Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa na jihar Katsina ya yi alƙawarin biyan kuɗin hadaya, Riyal 720 na ƙasar Saudiyya ga kowane mahajjaci daga jihar.

Raɗɗa ya kuma yi alƙawarin bayar da don Barka Sallah da aka saba yi ga alhazan jihar a ƙasa mai tsarki.

Gwamna Dikko Raɗɗa ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ƙaddamar da tawagar mutane 11 na jihar zuwa aikin Hajjin bana a ƙarƙashin jagorancin tsohon mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Tukur Ahmed Jikamshi.

KU KUMA KARANTA:Gwamnan Katsina ya saka hannu kan dokar haramta ɓoye abinci

Gwamnan ya umurci tawagar alhazai da hukumar kula da jin daɗin alhazai da su tabbatar da cewa ba a cire ko kobo ɗaya daga cikin guzurin alhazai ba.

Ya bayyana farin cikinsa cewa duk da ƙalubalen da ake fuskanta a sakamakon ƙarin kuɗin aikin Hajji da aka yi, alhazan jihar sun samu nasarar biyan kuɗin.

A cewarsa, tawagar jihar tana da hurumin kula da yadda za a gudanar da aikin Hajji daga farko zuwa ƙarshe a bana.

Leave a Reply