Tallafin dubu 5 da gwamnatin Najeriya ke bayarwa ya yi kaɗan – Bankin Duniya

0
67

Bankin Duniya ya bayyana tasirin tallafin Naira dubu 5 da gwamnatin tarayyar Najeriya ke rabawa a matsayin marar yawa ga buƙatun iyalai da harkokin banki.

Bankin Duniyar ya bayyana haka a rahotonsa na baya-bayan nan, mai taken, “alheri ya zo” ko “beta don come” a turancin broka: tasirin ba da tallafin kuɗaɗe akan mata da iayalai a Najeriya”.

A cewar rahoton, tallafin na da taƙaitaccen tasiri akan sana’o’i, Musamman ma akan mata.

Rahoton ya ba da misalin da shirin ba da tallafin kuɗaɗe na shekarar 2016, sa’ilin da gwamnatin tarayyar Najeriya ta ƙaddamar da shirin ba da tallafinta na NASSP.

KU KUMA KARANTA:Bankin Musulunci zai ba da $418m ga Tajikistan, Benin, Ivory Coast, da Turkiyya

A yayin ƙaddamar da shirin, rahoton yace gwamnatin tarayyar ta samarwa iyalai tallafin Naira dubu 5, inda ake ba da su a dunƙule duk bayan wata biyu.

Rahoton ya ƙara da cewar, ana biyan kuɗaɗen tallafin ne ta hannun waɗanda ragamar kulawa da iyalan ke hannunsu, galibinsu mata.

Saidai rahoton ya ba da shawarar cewar akwai buƙatar samun wata sana’ar da za ta riƙa tallafawa tallafin domin inganta samu da dogaro da kan iyalan.

Bankin Duniyar ya ƙara da cewar duk da nasarar da ake iƙirarin shirin bada tallafin kudaden ya samu, babu wata shaida ko guda dake nuna tasirin kasancewa a cikinsa.

Leave a Reply