An ji harbe-harben bindiga a birnin N’djamena na Chadi

0
112

Hukumomin a Chadi sun ba za dakaru a sassan ƙasar musamman a N’djamena, babban birnin ƙasar, a wani mataki na kwantar da duk wata tarzoma da ka iya tashi, bayan da aka sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasar da aka yi a ranar 6 ga watan Mayu.

A wani abu na bazata, hukumar zaɓen ƙasar ta sanar da sakamakon a daren Alhamis inda Shugaban mulkin sojin ƙasar Janar Mahamat Idriss Deby ya lashe zaɓen da kashi 61 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa.

Sai dai babban abokin hamayyarsa Succes Masra na ikyirarin shi ya lashe zaɓen da kashi 73 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa.

Da safiyar Juma’a al’ummar birnin ta N’djamena ta wayi gari da jin ƙarar harbe-harben bindiga.

Wani mazaunin birnin mai suna Oumar ya ce mai yiwuwa gwamnatin ta Chadi ce ta ba da umarnin yin harbi a wani mataki na tsorata masu adawa da sakamakon zaɓen.

An dai fitar da sakamakon zaɓen mako guda gabanin wa’adin da aka yi tsammanin za a sanar da shi.

Alƙaluman zaɓen sun nuna cewa Deby Itno ya samu kashi 61 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa, yayin da Masra ya samu kashi 18.5 cikin 100.

Tun gabanin sakin sakamakon Masra ya yi zargin cewa an tafka maguɗi.

KU KUMA KARANTA:An ayyana Mahamat Idriss Deby a matsayin wanda ya lashe zaɓen Chadi

Zaɓen na Chadi ya wakana ne bayan shekaru uku da ƙasar ta zauna ƙarƙashin mulkin soji.

Tun da farko dama masu fashin baƙi sun yi hasashen cewa Shugaba Deby Itno ne ake sa ran zai lashe zaɓen wanda ‘yan takara goma suka fafata ciki har da mace ɗaya.

A shekarar 2021 Shugaba Itno ya karɓi ragamar mulkin ƙasar daga hannun mahaifinsa da aka kashe a fagen daga, wanda ya kwashe shekru sama da 30 yana mulki.

Hukumar zaɓen ƙasar ta ce mutum miliyan 8.2 ne aka yi rijista don kaɗa ƙuri’arsu a wannan zaɓe wanda aka tura dakarun ƙasar sama da dubu 26 su kare rumfunan zaɓe.

Leave a Reply