No menu items!

Sample Page Title

Date:

Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da hukuncin kisa ga masu safarar miyagun ƙwayoyi a ƙasar.

Wannan na zuwa ne bayan nazarin rahoton kwamitocin da ke kula da ɓangaren shari’a, ‘yancin ɗan Adam da al’amuran shari’a da miyagun ƙwayoyi da magunguna da ke karkashin Dokar Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA)  da aka yi wa kwaskwarima a 2024.

Shugaban Kwamitin, Sanatan Borno ta Arewa Mohammed Monguno na jam’iyyar APC ne ya gabatar da rahoton yayin zaman majalisar a ranar Alhamis.

Kudirin dokar wanda ya tsallake karatu na uku, yana da nufin sabunta jerin miyagun ƙwayoyi masu haɗari, da ƙarfafa ayyukan hukumar ta NDLEA, da sake duba hukuncin da za a yanke ga masu fataucin miyagun ƙwayoyi da kuma ba da damar kafa ɗakunan gwaje-gwaje.

KU KUMA KARANTA: NDLEA ta kama gungun masu safarar miyagun ƙwayoyi zuwa Amurka da Turai

Sashi na 11 na dokar da aka yi a yanzu ya tanadi hukuncin ɗaurin rai da rai ga masu safarar miyagun ƙwayoyi da kotun da ke da hurumi ta same su da laifin. Sai dai ƙudirin dokar na 2024 ya nemi a tsananta hukunci mai tsauri wanda shi ne kisa.

Kodayake rahoton bai bayar da shawarar yanke hukuncin kisa kan laifin ba, inda a yayin nazarin ƙudirin, Sanata Ali Ndume ya yi nuni da cewa a tsananta hukuncin ɗaurin rai da rai zuwa hukuncin kisa.

A yayin da aka yi la’akari da wani sashi na ƙudirin, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, wanda ya jagoranci zaman na wannan Alhamis ɗin, ya tabbatar da ɗaukar hukuncin kisa ga masu laifin fataucin miyagun ƙwayoyi yayin da mafi rinjayen mambobin majalisar suka kaɗa ƙuri’ar baka ta amincewa da hukuncin.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...