Shugaban Turkiyya ya gana da jami’an tsaron Poland da Romania a Ankara

0
95

Shugaban Ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya karɓi baƙuncin shugaban tsaron ƙasa na Poland Jacek Siewiera da mai bayar da shawara kan sha’anin tsaro na Romania Ion Oprisor a Ankara.

An gudanar da ganawar a fadar shugaban ƙasa da ke Ankara a ranar Laraba inda aka yi duba kan haɗin kan tsaro a tsakanin ƙasashen da yaƙin Ukraine, tare da rikicin baya-bayan nan na Isra’ila da Falasɗinu, in ji sanarwar da sashen sadarwa ya fitar ta shafin X.

Da yake bayyana cewa matakan da Ankara ke ɗauka kan yaƙin Ukraine irin na Poland da Romania ne, shugaba Erdogan ya ƙara da cewar ba a samu wani cigaba ba wajen samar da zaman lafiya, duk da shafe fiye da shekara biyu ana gwabza yakin.

Da yake bayyana buƙatar buɗe kofar da za ta samar da hanya mai kyau ga ɓangarorin biyu, Erdogan ya ce matakin samar da zaman lafiya na ɓangare ɗaya da ba zai yi aiki da Rasha ba yana da rauni wajen samun nasara.

KU KUMA KARANTA: Turkiyya ce ta aika da kayan agaji  mafi yawa zuwa Gaza da ya kai tan 50,000 — Erdogan

Shugaba Erdogan ya ce ta’addancin Isra’ila a Gaza ya tsananta, yana mai kara wa da cewa lamarin ba jarrabawa ce ga tsaro ba kawai, har ma ga mutuntaka.

Shugaban na Turkiyya ya kuma ce Isra’ila na ci gaba da kisan kare dangi, duk da nuna buƙatar tsagaita wuta da Hamas ta yi, yana mai jaddada cewar irin matakan da aka ɗauka a Ukraine ya kamata a dauka a Gaza.

Sanarwar ta ce “Shugaba Erdogan, wanda ke bayyana fatan da Turkiyya take da shi a taron NATO da za a gudanar a Washington, ya ce fatan ya haɗa da ganin an tabbatar da cikakken goyon baya ga NATO, kawaye su daina saka wa juna takunkumai, sannan a daina kokarin mayar da Ankara saniyar-ware a harkokin NATO da Tarayyar Turai”.

Daraktan Sadarwa Fahrettin Altun, da Mai Bayar da Shawara ga Shugaba Erdogan Akif Cagatay Kili da sauran manyan jami’an gwamnati sun halarci ganawar.

Leave a Reply