’Yan sanda sun tsare ’yan canji 17 a kasuwar WAPA

0
123

’Yan sanda da jami’an hukumar DSS sun kama ’yan canji guga 17 a kasuwar canjin kuɗaɗe ta WAPA da ke Kano kan zargin ba su da rajista.

Kwamishinan ’Yan sandan jihar Kano, Usaini Gumel, ya sanar a ranar Laraba cewa waɗanda aka kaman ba su da lasisin gudanar da hadahadar canjin kuɗaɗe.

“Mun gudanar da aiki tare da hukumar tsaro ta DSS a kasuwar canjin kuɗaɗe ta WAPA inda jami’anmu da suka kama mutane 29, amma daga bisani aka saki 12 daga cikinsu.

“Mun kama su da kuɗaɗe da suka haɗa da Sefa 68,000 CFA da kuma Rupee 30 na ƙasar India.

KU KUMA KARANTA: Soke lasisin dubban kamfanonin canji ba zai kawo maslaha ba – ‘Yan Canji

“Duk wanda ake zargin sun amsa laifin kuma za a gurfanar da su a gaban kotu,” in ji kwamshinan an sandan.

A cewarsa, “Mun gudanar da samamen ne domin kawar da ɓata-garin da gudanar da harkar canjin kuɗi ba bisa ƙa’ida ba, waɗanda ke sa harkar tangal-tangal a ƙasar nan.”

Leave a Reply