Putin ya fara wa’adi na biyar a karagar mulkin Rasha

0
164

Vladimir Putin na fara zango na biyar a kan mulkin Rasha bayan wani biki na ƙasaita da aka gudanar a ranar Talata a Fadar Cremlin, bayan ya rusa abokan hamayyarsa na siyasa tare da samun cikakken ƙarfi a hannuna.

Tuni ya kwashe kusan shekaru 25 a kan mulki kuma wanda ya fi kowa daɗewa a mulkin Fadar Cremlin bayan Josef Stalin, Putin zai kammala wannan wa’adi a shekarar 2030, kuma bayan nan kundin tsarin mulki ya ba shi damar sake tsayawa takara da yin wani wa’adin na shekaru shida.

Bayan fara yaƙin Ukraine a 2022 wanda ya zama yaƙi mafi girma a Turai tun bayan Yaƙin Duniya na II, ƙasashen Yamma sun kakaba wa Rasha takunkumai, kuma ta koma mu’amala da kasashe irin su China, Iran da Koriya ta Arewa don neman goyon baya.

Abin tambaya a nan shi ne me Putin dan shekara 71 zai yi a sabon wa’adin mulki na shekaru shida, a cikin gida da wajen ƙasar?

KU KUMA KARANTA: Birtaniya ta tura wa Ukraine ƙunshin makamai mafi girma don yaƙar Rasha

Dakarun Rasha na samun ƙarfin mamaya a Ukraine, na amfani da dabaru a lokacin da Kyiv ke fama da ƙarancin mayaƙa da makamai. Dukkan ɓangarorin biyu na tafka babbar asara.

Ukraine ta kai yaƙin zuwa yankunan Rasha ta hanyar amfani da jiragen yaƙi marasa matuƙa da makamai masu linzami, musamman a hare-haren yankunan da ke kan iyaka.

A wani jawabi da ya yi a watan Fabrairu, Putin ya yi alkawarin cika manufofin Moscow a Ukraine, sannan zai yi duk mai yiwuwa don kare martaba da ‘yancin Rasha tare da samar da tsaron kasa.

Jim kaɗan bayan sake zaɓar sa a watan Maris, Putin ya bayyana cewa akwai yiwuwar a yi fito na fito tsakanin NATO da Rasha, kuma ya bayyana yana son samar da yankin samun kariya a ƙasar Ukraine don kare ƙasarsa daga harin kan iyaka.

A cikin gida, farin jinin Putin ya ta’allaka ne ga yadda ya inganta rayuwar al’ummar Rasha a yayin da tattalin arzikin ƙasar ke bunƙasa.

Ya fara wa’adin daya kammala a 2018 ta hanyar yin alƙawarin zai sanya Rasha zama daya daga cikin kasashe biyar mafiya ƙarfin tattalin arziki a duniya, yana mai cewa hakan zai zo a zamanance ta hanyoyi daban-daban.

Sai dai kuma Rasha na kashe makudan kuɗaɗe a ɓangaren tsaro.

Manazarta na cewa a yanzu da Putin ya samu damar ƙara yin wa’adi na shekaru shida a kan mulki, gwamnati na iya ɗaukar matakan da ba za a so ba na ƙara haraji don ɗaukar nauyin yakin da ake yi, tare da taƙura wa maza su shiga aikin soji.

A farkon fara sabon wa’adi, Putin ya rusa majalisar zartarwar gwamnatinsa ta yadda zai sanar da sabon Firaminista da majalisar ministoci.

Wani ɓangare da ake ta kallo shi ne ma’aikatar Tsaro.

A shekarar da ta gabata Ministan Tsaro Sergei Shoigu ya fuskanci matsin lamba kan yadda yake kula da yakin, inda shugaban ‘yan bindiga Yevgeny Prigozhin ya dinga sukarsa saboda karancin makamai ga mayakan da suka dauka haya don yaki a Ukraine.

Tawyen da Prigozhin ya yi a watan Yuni don adawa ga Ma’aikatar Tsaro ya zama babbar barazana ga mulkin Putin.

Bayan an kashe Prigozhin a hatsarin jiragen sama da watanni biyu, sai aka fahimci Shoighu ya yi nasarar cin yakin.

Amma a watan da ya gabata, an zargi yaronsa kuma mataimakin Ministan tsaro Timur Ivanov da hannu a ayukan cin hanci da rashawa.

Wasu masu nazari na cewa Shoigu na iya zama wanda sauyin ministoci zai iya shafa, amma hakan zai zama babban mataki saboda ana ci gaba da gwabza yaki a Ukraine.

Babban makiyin putin a siyasa, Alexei Navalny ya rasu a Arctic da ake tsare da shi a watan Fabrairu.

Leave a Reply