An shawarci Najeriya kan fara noman macizai

0
59

Dafin maciji ya fi gold tsada a kasuwa

Daga Idris Umar, Zariya

A ciki satin da ya gabata ne wakilinmu ya ziyarci shahararren mutumin nan mai sana’ar kiwon maciji a ƙasar Zazzau wato Idris Umar, Zariya akan harkar kiwon macizai da yake yi a halin yanzu.

Da farko bayan ya yi godiya da ziyarar, ya kuma bayyana yadda yake rayuwa da macizai a gidansa dare da rana sannan kuma ya baiwa gwamnatin Najeriya shawara da su ƙirkiro da hanyar da za a fara kiwon macizai a gwamnatance ba tare da wani tsoro ba.

Malamin yace, har yanzu ba a sami wani ma’adani da ya kai dafin maciji daraja ba a kasuwance a duniya baki ɗaya.

Mai macizai yace, daga cikin baiwar da Allah ya yiwa maciji shi ne, maciji ba ya wabi kamar yadda sauran dabbobi suke yin wabi.

Ya ce, maciji yakan yi ƙwai guda ɗari (100) a lokaci guda kuma ya ƙyanƙyashe su baki ɗaya.

Da Malam Idris ke bayyana sirrorin da dafin maciji yake da shi wanda ɗan adam ke amfani da shi a rayuwarsa ya fara da cewa, dafin maciji ana amfani da shi wajen haɗa manyan makamai da ake amfani dasu a duniyar (science) wato (makaman ƙare dangi) da ake yaƙe-yaƙe dasu duk da dafin maciji ake haɗa sinadaran.

Yace, ana haɗa magunguna dashi kala-kala da suka shafi kansa.

Malamin ya tabbatar da cewa dukkan matsalar da ake samu na rasa rayuka a jihohi kamar jihar Gombe /Kaltungo da jihar Filato/Ɓilliri sakamakon cizon macizai wanda da gwamnati ta faɗaɗa tunani akan kiwon macizai da an samu sauƙin matsalar da take addabar mutanen yankin.

Yace, dalili shi ne, ita allurar da ake yiwa duk wanda maciji ya sara ko ya caka a duk faɗin duniya da dafin maciji ake haɗata a kimiyyar scientist na duniya.

Malamin yace, yanzu haka a ilmin science kowane maciji idan ya yi cizo da irin alluran da ake yiwa mutum domin kowane maciji da irin alluran sa.

Malam Idris Umar

Yace amma tambaya anan shi ne idan maciji ya yi cizo a cikin dare bayan ya yi cizon sai ya gudu ya za ayi da wanda macijin ya ciza?

Gashi a doka ba zai yiwu bakin maciji ya yi cizo sai likita ya yi maka allurar da ba na bakin maciji ba hakan haɗari ne babba.

Mafita shi ne gwamnati ta fito da hanyar faɗaɗa kiwon macizai hakan zai sa a samu ƙwararru likitoci a fannin da za su iya ƙirƙiro magunguna daban-daban da za su taimakawa al’umma ƙasa baki ɗaya.

Daga ƙarshe mai macizai yace idan gwamnati ta ƙikiro kiwon macizai za a samu likitoci a fannin wanda hakan zai bayar da damar samun bincike akan yadda za a haɗa maganin cizon maciji cikin sauƙi.

Kuma idan gwamnati ta fara kiwon macizai za ta samu kuɗin shiga mai tsoka domin dafin maciji yafi zinari kuɗi a kasuwar duniya.

Bisa haka mai macizai ya yi ƙira ga gwamnati da ta fara fito da hanyar noman macizai kuma ya shawarci ɗaliban Ilimi da su karanci kimiyyar maciji saboda ƙarancin likitocin a fannin.

Bincike ya tabbatar da cewa dafin macijin yafi gold tsada a ka kasuwar duniya

Amma kuma wani bincike ya nuna mutane da yawa suna rasa rayuka akan matsalar rashin maganin cizon macijin a dukkan asibitocin dake ƙarƙashin gwamnatin tarayya dana jihohi zuwa ƙananan hukumomi.

A lokacin gwamnatin marigayi Janaral Sani Abacha an samu ci gaba inda gwamnatinsa ta fitar da wani tsari haɗin guiwa tsakanin ƙasar United Kingdom (Ingila) da ƙasar Najeriya da aka yi tsarin bani Gishiri in ba ka Manda wato Najeriya na baiwa (United Kingdom) macizai su kuma United Kingdom sai su ba Najeriya magani da suka haɗa ƙarƙashin Federal Ministry of Health tare da kafa wata cibiyar mai suna Anti Snake and venom study Group (UKvsNIG). Ƙarƙashin Dakta Abdul-Salam Nasidi.

Wannan shirin ya taimaki al’ummar Najeriya sosai.

Leave a Reply