Rarara ya faɗi matsayin Aisha Humaira a wajensa

0
130

An daɗe ana yamaɗiɗin cewa Rarara da Humaira na soyayya inda aka riƙa haɗa hotunansu ana cewa suna shirin aure.

Fitaccen mawaƙin Hausa Dauda Kahutu Rarara ya ce alaƙa da ke tsakaninsa da jaruma Aisha Humaira ba ta wuce ta amince da yarda ba.

Amma yayin hirar da ya yi da Freedom Radio, Kano a shirin “Daga Kannywood,” Rarara ya ce babu batun soyayya a tsakaninsa da jarumar.

KU KUMA KARANTA:An kori ‘yan sandan dake tsaron Rarara saboda wasa da alburusai

“Matsayin Aisha, ita ce ta uku a ofis ɗinmu (a muƙami,) daga ni sai Aminu sai ita, babu wani abu da ya wuce wannan.

“Yadda take a jadawali na kamfani, musamman nawa, akwai aminci da yarda akwai kuma mu’amulla mai kyau.” In ji Rarara.

Ya ƙara da cewa, “ina faɗa zan ƙara maimaitawa, ita (Aisha) duk wanda yake mu’amulla da ita a industry (Kannywood) sai dai ya zalunce ta, ko da rigima ka ga ana yi da ita yawanci ita ce mai gaskiya. Kuma a ita ce mai gaskiyar za ta ce ta haƙura. Duk wani furodusa ko darekta babu wanda zai ce maka ya taɓa faɗa da Aisha.”

Leave a Reply