Gwamnatin tarayya za ta fara farautar ma’aikatan da suke da shaidar karatun bogi

0
104

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za ta fara farautar ma’aikatan gwamnati da na ma’aikatu masu zaman kansu da ke aiki da takardun bogi.

Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamma ne ya bayyana hakan a jiya Juma’a a lokacin da ya karɓi rahoton kwamitin bincike na ma’aikatu kan takardar shaidar digiri na bogi daga shugaban kwamitin, Farfesa Jubrila Amin.

Mamman, wanda ya bayyana ɓacin ransa kan abin da aka gano a yayin gudanar da bincike, ya ce ma’aikatar za ta haɗa hannu da hukumomin da su ka dace domin tsaftace fannin ilimi da kuma kawar da duk wata ɗabi’a ta bogi.

KU KUMA KARANTA:Bamu da wani Farfesan bogi a Jami’ar Bayero – Shugaban Jami’ar

“Ba za mu bari wasu tsiraru gurɓatattu su ɓata harkar iliminmu ba. Mai yiyuwa ne wasu na aiki da takardun bogi a ma’aikatun gwamnati da masu zaman kansu, waɗanda ya kamata a yi farautar su.

“Wannan rahoto ya samo asali ne daga cikakken bincike,” inji shi.

Ya ce: “Abin takaici ne a ce wanda ya kamata ya fito daga wata jami’ar Najeriya da sakamakon 2:1 ko 2:2 amma sai ya samo shaidar dogiri na ƙarya kuma ya ci maki mafi girma, to ba za mu lamunta ba,” in ji shi.

Leave a Reply