Kotun duniya ta ICJ ta yi watsi da buƙatar hana Jamus fitar da makamai zuwa Isra’ila

0
149

Alkalai a kotun ƙasa da ƙasa sun yanke hukuncin ƙin bayar da umarnin gaggawa na dakatar da safarar makamai da Jamus ke fitarwa zuwa Isra’ila, inda suka ƙara da cewa sun damu matuka game da yanayin Gaza.

Sai dai kuma Kotun ba ta amince da bukatar Jamus ta yin watsi da shari’ar ba, don haka za a ci gaba.

Tun da fari ƙasar Nicaragua ce ta shigar da buƙatar neman a hana Jamus shigar da makaman zuwa Isra’ila, a yayin da Isra’ilan ke ci gaba da yaƙi a Gaza.

Leave a Reply