‘Yan Houthi sun yi iƙirarin kai hari kan jiragen ruwa 4, ciki har da na Amurka 2

0
80

Kakakin rundunar Houthi Yahya Sarea ya bayyana a wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin cewa ‘yan tawayen Houthi na kasar Yemen sun kai hari kan jiragen ruwa guda biyu na Amurka da kuma jirgin CYCLADES a Bahar Maliya da kuma MSC Orion da ke gabar Tekun Indiya.

“Dakarun Yemen sun kai farmakin soji kan jiragen ruwan yaƙi da suke mana barazana a Bahar Maliya, inda harin na jirage marasa matuƙa ya sauka a kan jiragen yaƙin Amurka guda biyu. An cimma nasara a manufofin sojin,” in ji Sarea.

KU KUMA KARANTA: Mayaƙan Houthi sun kai wa jirgin ruwan Amurka hari a Bahar Maliya

“Harin da aka kai wa jirgin ya zo ne bayan da ya karya dokar hana zirga-zirgar jiragen ruwa zuwa tasoshin ruwa na Falasdinu da aka mamaye, a kan hanyarsa ta zuwa tashar jiragen ruwa ta Umm al-Rashrash a ranar 21 ga Afrilu, inda ya yi amfani da salon yaudara da cewa yana kan hanyarsa ta zuwa wata tashar ruwan ne daban,” in ji shi.

Sojojin Houthi sun kwashe tsawon watanni suna kai hare-hare kan hanyoyin jiragen ruwa domin nuna goyon bayansu ga Falasdinawa na Gaza a daidai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kashe-kashe a Gaza.

Leave a Reply