No menu items!

Sample Page Title

Date:

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa na zuba jari matuƙa a ɓangaren fasaha wadda za ta taimaka wurin kawo ci gaba ga gwamnatin Najeriya.

Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin wata tattaunawa da shugaban kamfanin Microsoft wato Bill Gates, bayan sun haɗu a birnin Riyadh na Saudiyya a ranar Lahadi.

Shugaban ya bayyana cewa fasaha ta kasance wani makami da ake amfani da shi domin yaƙar cin hanci da rashawa da kuma yaƙar yadda ake wadaƙa da kuɗaɗen al’umma.

Tinubu ya jaddada cewa ana samun turjiya daga wurin al’umma a yunƙurin da ake yi na amfani da fasaha wurin kawo ci gaba.

KU KUMA KARANTA: Ta’addanci babbar masifa ce da aka shigo da ita Afirka daga waje – Shugaba Tinubu

“Fasaha abokiyar gaba ce ga cin hanci da aikata ba daidai ba. Muna ta aiki tuƙuru domin inganta fasaha,” in ji Shugaba Tinubu.

Shugaban ya bayyana cewa lokacin da yake gwamnan Legas, ya yi amfani da fasaha domin tattara bayanai da kuma amfani da su wurin karɓar haraji, wanda hakan ya samar da tsari mai kyau na karɓar haraji.

A martanin da ya mayar, Mista Gates ya shaida wa shugaban ƙasar kan cewa akwai wata manhaja ɗaya wadda za a iya amfani da ita wurin haɗe bayanai da suka shafi tsare-tsare da tsaro da kuma kula da haraji.

“Muna aiki tare da Mista Wale Edun, wanda shi ne Ministan Tattalin Arziki da Kuɗi kan batun fasahar zamani. Kafin ka karɓi mulki, akwai wasu abubuwa kaɗan da aka yi ƙoƙarin haɓaka manhajar tattara bayanai. Sai dai an bar su sun warwatsu. Akwai manhajoji da dama na tantance bayanan mutane.

“A yanzu akwai shirin da ake yi na amfani da fasahar nan ta MOSIP wurin tattara bayanai ta yadda jama’a za su iya samun abubuwansu ta yanar gizo. Za mu iya taimakawa ta wannan ɓangaren kuma za mu iya bayar da ƙarin taimako,” in ji Bill Gates.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...