An kashe ‘yan ƙato-da-gora 23 a Borno da Sokoto

0
117

An kashe ‘yan ƙato-da-gora aƙalla 23 a hare-hare daban-daban da ‘yan bindiga da masu tayar da ƙayar baya suka kai musu a jihohin Borno da Sokoto a ƙarshen makon da ya wuce, kamar yadda jami’ai suka bayyana ranar Lahadi.

A jihar Borno, ana zargin mayaƙan ƙungiyar ISWAP ne suka dasa nakiyoyin da suka tashi a cikin wata mota da ke ɗauke da ‘yan ƙato-da-gora waɗanda aka fi sani da sibiliyan JTF, kamar yadda shugabansu ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Reuters. Lamarin ya faru ne ranar Asabar.

Tijjanima Umar, shugaban CJTF na yankin Gamboru Ngala, ya ce motar jami’ansu tana kan hanyar zuwa Maiduguri lokacin da nakiyoyin suka fashe inda suka kashe ‘yan ƙato-da-gora da yawa.

“Bayan nakiyar ta fashe, nan-take mambobinsu tara suka mutu… yayin da biyu kuma suka ji munanan raunuka inda aka garzaya da su asibiti,” in ji Umar.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta umarci ‘yansanda su biya diyyar naira miliyan 300 bisa kashe ‘yan Shi’a 3 a Zariya

Duk da yake sojojin Najeriya da ‘yan ƙato-da-gora sun ci ƙarfin mayaƙan Boko Haram da ISWAP da ska addabi arewa maso gabashin ƙasar, har yanzu suna kai hare-hare jefi-jefi kan fararen-hula da jami’an tsaro.

A gefe guda, ‘yan bindiga sun yi kwanton-ɓauna ga ‘yan sibiliyan JFT a Sokoto ranar Asabar, inda suka kashe 14 daga cikinsu, a cewar kwamandansu Ismail Haruna a hirar da ya yi da Reuters ta wayar tarho.

Haruna ya ce lamarin ya faru ne a ƙaramar hukumar Isa, inda suka kai samame a maɓoyar wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane.

A cewarsa, ‘yan bindigar sun yi sauri suka haɗa kai sannan suka yi wa ‘yan sibiliyan JTF a yayin da suke kan hanyarsu ta komawa Sokoto.

Arewacin Najeriya ya daɗe yana fama da matsalolin tsaro iri-iri ciki har da satar mutane don neman kuɗin fansa da hare-haren ’yan bindiga da rikicin manoma da makiyaya da sauransu.

A makon jiya ne kamfanin Beacon Consulting da ke nazari kan harkokin tsaro ya fitar da wasu alkaluma, inda ya ce an kashe mutum 2,583 kuma sace mutum 2,164 a faɗin Najeriya a watanni uku na farkon wannan shekarar.

Ya ce kashi 80 cikin 100 na kashe-kashe da kuma kaso 94 cikin 100 na garkuwa da mutane sun samu faru ne a yankin arewacin ƙasar.

Leave a Reply