No menu items!

Sample Page Title

Date:

Kamfanin fito na ƙasar Denmark, A.P. Moller-Maersk, ya amince ya zuba jarin $600m a tashoshin jiragen ruwa na Nijeriya, kamar yadda fadar shugaban ƙasar ta bayyana ranar Lahadi.

A.P. Moller-Maersk ya ayyana aniyar zuba jarin ne a ganawar da Shugaba Bola Tinubu ya yi da shugabansa Robert Maersk Uggla a gefen taron kasuwanci na World Economic Forum da aka gudanar a birnin Riyadh na Saudiyya.

“Mun yi amanna da Najeriya, kuma za mu zuba jarin $600m a tashoshin jiragen ruwan ƙasar yadda manyan jirage za su samu damar zuwa,” in ji Mr Uggla.

Shugaba Tinubu ya ce jarin da kamfanin zai zuba a tashoshin jiragen ruwan ƙasar zai ƙarfafa jarin dala bilian ɗaya da tuni aka sanya wajen inganta tashoshin jiragen ruwa a gabashi da yammacin Nijeriya.

Gwamnatin Najeriya ta yi alƙawarin inganta tashoshin jiragen ruwan ƙasar, ciki har da waɗanda suke birnin Legas, cibiyar kasuwancin ƙasar, domin sauƙaƙa harkokin kasuwanci.

“Muna buƙatar ƙarfafa gwiwar ‘yan kasuwa da dama domin faɗaɗa hanyoyin samun kuɗaɗen shiga da rage kwashe kayayyaki daga manyan jirage zuwa ƙanana,” in ji Shugaba Tinubu.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...