Gwamnan Kebbi ya ba da tallafin naira miliyan 309 a ɗaliban da ke karatu a ƙasashen waje

0
96

Daga Idris Umar, Zariya

Gwamna jihar Kebbi Nasir Idris ya ba da umurnin biyan Naira miliyan 309.5 domin biyan tallafin Kuɗaɗen karatu ga ɗalibai ‘yan asalin jihar Kebbi da ke karatu a ƙasashen Indiya da masar su 86.

Kwamishinan ma’aikatar ilimi mai zurfi ta jihar Malam Isah Abubakar-Tunga ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Birnin Kebbi.

KU KUMA KARANTA: Ƙungiyar tallafawa marayu ta Jama’atul Nasirul Yatama Kudan ta baiwa marayu tallafi

Ya ce, “Gwamna Nasir Idris ya biya kuɗin tallafin karatu na ƙasashen waje ga ‘yan asalin jihar Kebbi da ke karatu a Indiya da Masar har Naira miliyan 228.1 ga ɗalibai 63 a Indiya da kuma Naira miliyan 81.4 ga ɗalibai 23 da ke a ƙasar Masar, inda ya bayar da tallafin karatu ga ɗalibai 23 a kasar Masar. jimillar Naira miliyan 309.5, in ji shi.

Ya ƙara da cewa sauran ɗaliban ƙasashen waje guda 50 nan ba da jimawa ba za a biya nasu kuɗaɗen su cikin ƙanƙanin lokaci da ikon Allah.

Ya kuma ƙara da cewa gwamnan ya biya duk ɗaliban jihar da ke karatu a manyan makarantu 36 a faɗin ƙasar nan tallafin karatu a watan Fabrairu, 2024.

Leave a Reply