Tinubu zai tafi ƙasar Netherlands

0
107

A yau Talata Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai bar Najeriya domin zuwa ƙasar Netherlands ziyarar aiki.

Kakakin shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale ya sanar cewa Tinubu ya amsa gayyatar da firaministan kasar Netherlands, Mark Rutte ya yi masa ne.

Ya ce daga Netherlands, Tinubu je taro na musamman kan Tattalin Arzikin Duniya (WEF) da aka shirya gudanarwa a ranakun 28 da 29 ga watan nan na Afrilu a birnin Riyadh na ƙasar Saudiyya.

Ngelale ya ce, yayin ziyarar a Netherlands, shugaba Tinubu zai tattauna da firaminista Mark Rutte, da kuma Sarki Willem-Alexander da Sarauniya Maxima.

Sarauniyar ita ce mai ba da shawara ta musamman ga Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya kan harkokin Kudi da cigabansu (UNSGSA).

KU KUMA KARANTA: Tinubu ya buƙaci ‘yan Najeriya su haɗa kansu don ciyar da ƙasar gaba

“Yayin ziyarar a ƙasar Netherlands, shugaban kasa zai halarci taron kasuwanci da zuba jari na ƙasashen biyu inda za su lalubo bangarorin hadin gwiwa da ƙarfafa juna, musamman a fannin noma da kula da dabarun kula da ruwa.

“Taron Kwamitin Tattalin Arzikin na Duniya zai mayar da hankali kan Haɗin gwiwa da hanyoyin kawo cigaban makamashi, inda Tinubu da mukarrabansa za su tattauna da mahalarta daga sauran ƙasashe a kan harkokin kasuwanci.

“Shugaban zai samu rakiyar wasu ministoci da wasu manyan jami’an gwamnatinsa,” inji Ajuri Ngelale

Leave a Reply