No menu items!

Sample Page Title

Date:

Chaina ta ce ta harba kumbon Long March 2D mai ɗaukar kaya, wanda ya kai tauraron ɗan’adam mai fasahar sansano nesa zuwa sararin samaniya.

An harba kumbon da ƙarfe 7:45 na safe (agogon Beijing) daga cibiyar Ƙaddamar da Kumbo ta Xichang, wadda ke gundumar Sichuan da ke kudu maso yammacin ƙasar.

Kumbon ya aika da tauraron ɗan’adam mai suna Yaogan-42 02 zuwa samaniya, a cewar kamfanin dillancin labarai na Xinhua News wanda ke mallakin gwamnati, ranar Lahadi.

Wannan shi ne karo na 17 a shekarar 2024, kuma karo na 517 na harba kumbo ajin Long March, wanda shi ne ƙasar take yawan amfani da shi cikin jerin kumbunanta.

KU KUMA KARANTA: Dole Chaina da Turkiyya su hana Iran kai harin ramuwar gayya a Isra’ila — Blinken

Kumbon samfurin The Long March 2D, yana amfani da makamashi na ruwa ne, kuma yana da ƙarfin ɗagawa da ya kai tan 300. Yana iya safarar kumbon da ke da nauyin tan-1.3 zuwa samaniya da ɗagawar kilomita 700.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...