Mun inganta hanyoyin tafiyar da gwamnatinmu – Gwamnan Zamfara

0
133

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya ƙara jaddada cewa gwamnatinsa ta kawo gagarumar gyara a hanyoyin tafiyar da gwamnati don samar da ci gaba mai inganci a jihar.

A ranar Litinin ɗin nan ne Gwamnan ya bayyana haka a lokacin da ya ke jagorantar zaman Majalisar zartarwar jihar, wanda ya gudana a fadar gwamnati da ke Gusau.

Kamar yadda ya ke ƙunshe cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Kakakin Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya kuma bayyana cewa Gwamnan, wanda shi ne shugaban Majalisar zartarwar ya tunatar da sauran mambobin Majalisar irin ƙalubalen da ake fuskanta a sha’anin mulki don tsamo jihar daga halin da ta ke ciki.

KU KUMA KARANTA: Jiragen yaƙin Najeriya sun yi luguden wuta a sansanonin ƴan ta’adda a Zamfara

Sanarwar ta ce, bayan da Gwamnan ya kammala jawabin sa na maraba, sai aka shiga tattauna muhimman batutuwa don tabbatar da su.

Yayin gabatar da jawabi ga mambobin Majalisar, Gwamna Lawal ya jawo hankalin su kan cewa su kasance masu aiki tare, maimakon kowa ya koma yana harkar gaban sa.

“Ganin yadda muke fuskantar 28 ga watan Mayu na 2024, wanda ranar ce za mu cika shekara ɗaya a ofis, wajibi ne mu ƙididdige abubuwan da muka yi, ya muka sauke nauyin da al’ummar jiha suka ɗora mana, kuma me ya kamata mu yi mu inganta gudanar da ayyukan ci gaban ƙasa da more rayuwa, kamar yadda muka yi wa masu kaɗa ƙuri’a alƙawari a yayin yaƙin neman zaɓe.

“Wajibi ne mu bibiyi abin da muka yi don mu san a ina mu ke, wane shiri za mu yi. Mun yi ƙoƙari sosai wajen canja yanayin aikin gwamnati zuwa yadda ya kamata. Mun kasance masu sanya buƙatun jama’a a birbishin komai, mun sanya gabatar da gyara a harkar tafiyar da gwamnati, tare da inganta hanyoyin kasuwanci. Ba abu ne mai sauƙi ba, amma dai muna samun ci gaba ta hanyar da ta dace. Za mu ci gaba da fafatawa ta tanyoyi masu ma’ana waɗanda za su taimaka wajen samar da harkar shugabanci mai kyau, mai ma’ana ga al’ummar da suka zaɓe mu.

“Gwamnati za ta samu nasara ne idan kowannen ku ya yi aiki tare da juna, maimakon a ɗaiɗaiku, waɗanda aikin ku ya bambanta da na juna. Na sha faɗa cewa, wajibi ne ku yi aiki a tare, ku kauce wa kulle kan ku, sai ku kaɗai. Aiki a tare, ita ce kalmar, duk wanda ya saɓa, to ba ya daga cikin mu.

Leave a Reply