Yadda aka kama dilan makaman ’yan ta’adda a tashar mota a Taraba

0
125

Sojoji da ’yan banga sun cafke wani mai yi wa ’yan ta’adda safarar makamai a tashar mota ta Jalingo da ke Jihar Taraba.

Daraktan hulɗa da jama’a na rundunar,  Manjo Janar Onyema Nwachukwe, ya ce kama dillalin makaman ’yan bindigar ya kai ga cafke wasu ’yan ƙungiyarsa. 

Nwachukwe ya ce  abubuwan da aka a hannun wadanda ake zargin sun hada da bindiga mai sarrafa kanta, bindigar da aka kera a gida, mota kirar Peugeot, wayoyin hannu guda biyar da kuma tsabar kudi 45,000.

KU KUMA KARANTA: Ƙarancin ma’aikatan tsaro, makaman yaƙi na zamani, rashin horaswa ne matsalar murƙushe ta’a’ddanci a Nijeriya, daga Dahiru Suleiman Dutse

A sanarwar da ya fitar a ranar Litinin ta hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar soji ta shida, Laftanar Oni Olubodunde, ya ce a wani samame na daban, sojojin da ke sintiri a kauyen Miyande a Karamar Hukumar Takum sun kama wasu ’yan ta’adda guda biyu da suka boye wata bindigu a ƙarƙashin kujerar babur da suke hawa.

An kwato bindiga kirar AK-47, harsasai na musamman mai girman 7.62mm har guda biyar, da kuma babur a yayin wannan samame. 

Olubodunde ya ci gaba da cewa, sojojin sun amsa kiran gaggawa inda suka dakile wani yunkurin yin garkuwa da mutane a garin Zaki-Biam da ke Karamar Hukumar Zaki-Biam a Jihar Binuwe, inda a yayin musayar wuta suka kashe daya daga cikin masu garkuwa da mutane tare da kwato bindiga da harsashai masu girman 9mm.

Leave a Reply