Ministan Harkokin Wajen Turkiyya da Sakatare Janar na MƊD, Guterres, sun tattauna kan halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya

0
71

Ministan Harkokin wajen Turkiyya Hakan Fidan ya tattauna kan halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya da Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Antoniyo Guterres, a cewar majiyoyin diflomasiyyar Turkiya.

A wata tattaunawa ta waya ranar Litinin, Fidan da Guterres sun yi kuma tattauna kan halin da ake ciki a Gaza.

Batun Cyprus da safarar teku cikin aminci a Bahrul Aswad na daga cikin batutuwan da aka tattauna, a cewar majiyar.

Tehran ta kai hare-hare sama da 300 da makamai masu linzami da jirage marasa matuka a fadin kasar Isra’ila a yammacin ranar Asabar a matsayin ramuwar gayya kan harin da jiragen Tel Aviv suka kai kan karamin ofishin jakadancin Iran da ke Damascus babban birnin kasar Syria, a ranar 1 ga Afrilu inda dakarun kare juyin juya halin Musulunci bakwai, ciki har da janar-janar guda biyu suka mutu.

KU KUMA KARANTA: Turkiyya ta nemi a kai zuciya nesa bayan ramuwar gayyar da Iran ta yi kan Isra’ila

Dangane da abubuwan da suka faru a yankin gabas ta tsakiya,Turkiyya ta ce za ta ci gaba da kokarin hana afkuwar wani tsari da zai lalata zaman lafiyar yankin har abada da kuma haifar da rigingimu a duniya.

Ankara ta ce “tana sake aikewa da sakwanni ƙarara ga mahukuntan Iran da kuma ƙasashen yammacin duniya da ke da tasiri a kan Isra’ila, don yin ƙira ga kowa da kowa da ya kawo ƙarshen tashin hankalin”.

Leave a Reply