No menu items!

Sample Page Title

Date:

Rahotanni sun nuna cewa Mohammed Idris ya faɗi kuma ya rasu jim kaɗan bayan kammala Sallar Idi a gidansa da ke Abuja ranar Laraba. Duk da ƙoƙarin farfaɗo da shi, Allah ya yi masa rasuwa.

Mohammed Idris, fitaccen jigo a siyasar Najeriya, kuma tsohon ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Ankpa, Olamaboro, da Omala na tarayya ya rasu.

KU KUMA KARANTA:Muƙarraban Ganduje sun mayar da martani kan kwamitin da Gwamnan Kano ya kafa na binciken tsohon gwamnan

Rasuwar Mohammed, wanda kuma ɗa ne ga tsohon gwamnan jihar Kogi, Ibrahim Idris, ta bar giɓi a fagen siyasa musamman a jiharsa ta Kogi.

A bisa al’adar Musulunci, an yi jana’izar Mohammed Idris a maƙabartar Gudu da ke Abuja bayan sallar jana’izar tare da halartar ɗimbim jama’a a babban masallacin ƙasa, tare da ‘yan’uwa, abokai, abokan aiki, da sauran jama’a.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...