No menu items!

Sample Page Title

Date:

A ranar Talata ake gudanar da ƙaramar sallah a Jamhuriyar Nijar bayan hukumomi sun bayyana ganin jaririn watan Shawwal.

Ranar Litinin da maraice Majalisar Ƙoli ta Addinin Musulunci ta Jamhuriyar Nijar ta ce an ga watan Shawwal a jihohi biyar na ƙasar.

Don haka ta bayar da umarni a gudanar da sallar idin ƙaramar sallah a ranar Talata, 1 ga watan Shawwal, 1445 daidai da 9 ga watan Afrilun 2024.

Majalisar Ƙoli ta Addinin Musulunci ta yi roƙon Allah ya karɓi ibadun da aka yi a watan Ramadan, sannan ta yi kira ga ƴan Nijar su ci gaba da yi wa ƙasar addu’o’in fatan alheri.

KU KUMA KARANTA: Ba a ga watan ƙaramar Sallah ba a Saudiyya

Sai dai ba a ga watan Shawwal ba a galibin ƙasashen duniya abin da ya sa hukumomi suka ayyana ranar Laraba, 10 ga watan Afrilu a matsayin ranar ƙaramar Sallah.

Ƙasashen da za su yi ƙaramar sallah ranar Laraba sun haɗa da Saudiyya da Falasɗinu da Najeriya da Qatar, da Iraƙi da Kuwait, da Masar, da Syria, da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

Wannan ne karo na farko da ƴan ƙasar Nijar za su yi bukukuwan ƙaramar sallah ƙarƙashin mulkin sojin na Janar Abdourahamane Tiani bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wa gwamnatin farar-hula ta Mohamed Bazoum a watan Yulin 2023.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...