Mutum 20 sun rasu a harin da RSF ta kai wani ƙauye na Sudan

0
140

Rundunar RSF ta Sudan ta kashe aƙalla mutum 20 a wani hari da ta kai wani ƙauye da ke kudancin Khartoum babban birnin ƙasar, kamar yadda wani kwamiti na ƴan gwagwarmaya a ƙasar ya tabbatar.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa RSF “ta kai hari kan ƙauyen Um Adam” mai nisan kilomita 150 daga Sudan a ranar Asabar, kamar yadda sanarwar da kwamitin ya fitar ta bayyana.

Yaƙi tsakanin sojojin Sudan ƙarkashin jagorancin Abdel Fattah al-Burhan da kuma rundunar RSF ƙarƙashin jagorancin Mohamed Hamdan Daglo ya soma ne 15 ga watan Afrilu.

An kashe dubban mutane, daga ciki har da wasu 15,000 da aka kashe a gari ɗaya a yankin Darfur, kamar yadda Majalisar Ɗinkin Duniya ta tabbatar.

Yaƙin ya kuma raba sama da mutum miliyan 8.5 da muhallansu tare da lalata ababen more rayuwa da dama da ke Sudan ɗin.

KU KUMA KARANTA: Ana zargin tsohon firaiministan Sudan Hamdok da laifin ‘tunzura’ mutane su yi yaƙi

Harin da aka kai a ranar Asabar ya yi sanadin “sama da mutum 200 sun samu rauni, sama da 20 kuma sun rasu,” in ji sanarwar.

Wata majiya daga asibitin Manaqil mai nisan kilomita 80, ta tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa sun karɓi “sama da mutum 200 waɗanda suka samu rauni, wasu daga cikinsu an yi jinkirin kai su”.

“Muna fuskantar ƙarancin jini kuma ba mu da isassun ma’aikatan lafiya,” kamar yadda majiyar ta ƙara da cewa.

Sama da kaso 70 cikin 100 na kayayyakin kiwon lafiya da ke Sudan ba su aiki, kamar yadda Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana, inda waɗanda suka rage kuma suna karɓar marasa lafiya fiye da yadda za su iya ɗauka.

Duka ɓangarorin da ke rikici da juna na zargin juna da aikata laifukan yaƙi, daga ciki har da kai hari kan fararen hula da buɗe wuta kan mai uwa da wabi da sace-sace da hana kai kayan agaji.

Tun bayan ƙwace iko da jihar Al-Jazira da ke kudancin Khartoum a watan Disamba, RSF ɗin ta ci gaba da yin ƙawanya da kai hari a duka ƙauyuka daga ciki har da Um Adam.

Zuwa watan Maris, aƙalla ƙauyuka 108 a faɗin ƙasar aka ƙona “ko dai baki ɗaya ko kuma wani ɓangare”, kamar yadda wata cibiya da ke bincike ta Birtaniya mai suna Centre for Information Resilience ta gano.

Leave a Reply