Shaikh Ɗahiru Bauchi na nan da ransa – Iyalansa

0
144

Daga Idris Umar, Zariya

Makusantan fitaccen Malamin Ɗarikar Tijjaniyya a Najeriya, Shaikh Ɗahiru Usman Bauchi sun ƙaryata jita-jitan da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta cewa babban malamin ya rasu.

Makusantansa sun ce labarin ƙanzon kurege ne, wanda bai da tushe balle asali.

Idan za a tuna a makon jiya ne aka yi ta yaɗa labarin cewa Shaikh Ɗahiru Usman Bauchi na fama da jinyar rashin lafiya mai tsanani, lamarin da ma makusantansa suka ƙaryata.

Sai kuma a ‘yan ƙwanakin nan masu yaɗa jita-jitan suka canza salo zuwa cewa ya rasu.

Da ya ke zantawa da manema labarai hadimin na kusa da Shaikh Ɗahirun, ya ce, “Maulana Shaikh yana cikin ƙoshin lafiya.

“Wasu ne kawai ke samun wuri su shirya ƙarya su yaɗa domin tayar wa jama’a da hankali. Amma lallai labarin ƙarya ne,”

Ɗaya daga cikin ‘ya’yan Shaikh Ɗahiru Usman Bauchi, Malam Abdallah ya wallafa a shafinsa na sada zumunci inda yake taya mahaifinsa murnar kammala tafsirin Alƙur’ani na bana.

Abdallah ya wallafa cewa, “Alhamdulillah muna taya maulana Shaikh murnar kammala tafsirin bana 2024 lafiya, da fatan Allah ya ƙara lafiya ya nuna mana na shekara mai zuwa. Shehu mungode!.”

Wannan dai ba shi ne karo na farko da ake yaɗa irin wannan jita-jitan ba, domin kuwa a lokuta baya ma an yaɗa cewa Shaikh Ɗahiru Usman Bauchi ya rasu alhali ƙaryane tsagwaronta.

Leave a Reply