Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya sanar da kama mutane 9 game da kisan jami’an ‘yan sanda a yankin Ughelli na jihar Delta.
Babban Sufeton ‘yansandan ya bayyana hakan ne yayin taron Hukumar Gudanarwar Rundunar a ranar Alhamis ɗin nan.
Ya ƙara da cewar, waɗanda aka kama ɗin na taimakawa rundunar da bayanan da za su kai ga kama mutanen dake da hannu a kisan.
A ranar 23 ga watan Fabarairun da ya gabata ne, aka hallaka jami’an ‘yansanda 6 a dajin Ohoro, da ke ƙaramar hukumar Ughelli ta Arewa a jihar Delta.
A wani labarin kuma, waɗansu mutanen 6 da ake zargi da hannu a kisan sun tsere.
KU KUMA KARANTA:’Yan fashi sun kai hari bankuna da ofishin ’yan sanda a Kogi
Kisan na zuwa ne a daidai lokacin da aka hallaka hafsoshin soja 17 a jihar ta Delta mai arziƙin man fetur.
An hallaka sojojin ne a yayin da suke aikin wanzar da zaman lafiya a ƙauyen okuama dake ƙaramar hukumar Ughelli ta Kudu a wani al’amari da ya janyo allawadai a faɗin Najeriya.
A yayin jana’izar sojojin da ya gudana a makon da ya gabata, hukumomin sojin Najeriya sun sha alwashin farauto waɗanda suka kitsa harin, tare da jaddada cewar hakan ba zai hana su cimma burinsu na fatattakar ɓata-gari daga faɗin Najeriya ba.
Haka shima, Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya miƙa lambobin girmamawar ƙasa ga sojojin da hallaka tare da ɗaukar nauyin karatun ‘ya’yansu.