Hamas ta shirya wa tsagaita wuta na dindindin a Gaza

0
108

Ƙungiyar gwagwarmayar Falasɗinawa ta Hamas ta ce ta sanar da masu shiga tsakani cewa za ta ci gaba da bin shawarwarinta na farko na cimma matsayar tsagaita wuta da ta hada da janye sojojin Isra’ila daga Gaza da kuma mayar da Falasɗinawan da suka yi gudun hijira zuwa yankunansu.

Har ila yau, ta buƙaci abin da ta ƙira “musayar fursunoni na gaske”, dangane da sakin fursunonin Falasɗinawa daga gidajen yarin Isra’ila domin musanya da Isra’ilawan da take garkuwa a Gaza.

Hamas ta gabatar da shawarar tsagaita wuta a Gaza ga masu shiga tsakani da Amurka a tsakiyar watan Maris da ta hada da sakin fursunonin Isra’ila da aka yi garkuwa da su domin samun ‘yanci ga fursunonin Falasɗinu, waɗanda 100 daga cikinsu ke zaman ɗaurin rai-da-rai, kamar yadda shawarar da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya gani ta bayyana.

KU KUMA KARANTA: Kwamitin Tsaro na MƊD zai sake kaɗa ƙuri’a kan tsagaita wuta a Gaza

Masar da Qatar dai na kokarin takaita bambance-bambancen da ke tsakanin Isra’ila da Hamas game da yadda yarjejeniyar tsagaita wuta ta kasance, sakamakon yadda matsalar jinƙai ke ƙara kamari da al’ummar Gaza ke fuskantar barazanar yunwa.

Hamas ta ce farkon sakin ‘yan Isra’ilan zai hada da mata da ƙananan yara da tsofaffi da marasa lafiya a matsayin wadanda aka yi garkuwa da su domin sakin Falasɗinawa 700-1000 da ake tsare da su a gidajen yarin Isra’ila, a cewar shawarar. An sanya batun sakin ”mata ƙanana sojoji” na Isra’ila a ciki.

Leave a Reply