Girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 6.9 ta auka wa ƙasar Papua New Guinea

0
153

Mutum aƙalla biyar ne suka mutu, kana an ƙiyasta gidaje 1,000 da suka ruguje a lokacin da wata girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 6.9 ta auka wa arewacin Papua New Guinea, kamar yadda jami’ai suka bayyana, yayin da ma’aikatan takaita aukuwar bala’o’i ke ta ƙoƙarin kai ɗauki yankin.

“Ya zuwa yanzu, an yi asarar kusan gidaje 1,000,” in ji Gwamnan Gabashin Sepik Allan Bird, yana mai ƙarawa da cewa ma’aikatan agaji “har yanzu suna kan aikin tantance tasirin iftila’in” da ya auku sakamakon girgizar ƙasa da ta “lalata sassa da dama na lardin.”

Mafi yawan ƙauyukan da ke gaɓar kogin Sepik na ƙasar sun jima suna fuskantar ambaliyar ruwa kafin girgizar ƙasar da ta afku a safiyar ranar Lahadi.

KU KUMA KARANTA: Girgizar ƙasa ta kashe sama da mutane 100 a arewa maso yammacin China

Kwamandan ƴan sanda na Lardin Christopher Tamari ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP cewa hukumomi sun sami labarin mutuwar mutane biyar amma akwai yiwuwar ”adadin ya wuce hakan”.

Hotunan da aka ɗauka bayan girgizar ƙasar sun nuna yadda iftila’in ya lalata gidajen katako waɗanda ambaliyar ruwa ta yi awon gaba da su.

Girgizar ƙasa ta zama ruwan dare a Papua New Guinea sakamakon zaman ƙasar a yankin ”Ring of Fire”, wurin da ke shimfiɗe a kan kusurwa duniyar Earth wanda ya mamaye kudu maso gabashin Asiya da yankin Pacific.

Ko da yake ba kasafai ake samun ɓarnar girgizar ƙasa a cikin tsaunin manyan dazuzzuka ba, amma suna iya haifar da zabtarewar ƙasa.

Yawancin ƴan ƙasar mutum miliyan tara, mai cike da tsibirai, suna zaune a wajen manyan garuruwa da birane, inda mafi yawan lokuta rashin hanya mai kyau kan iya janyo musu cikas ga ƙoƙarin ceto.

Leave a Reply