Connect with us

Labarai

El-Rufai ya sake ganawa da jiga-jigan jam’iyyar SDP a Abuja

Published

on

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna ya sake ganawa da waɗansu jiga-jigan jam’iyyar SDP a gidan Sanata Abubakar Gada tare da shugaban jam’iyyar na kasa Shehu Musa Gabam.

Wannan zama dai shi ne kusan na uku a kasa da kwana goma tun da El-Rufai ya fara bayyana a wani taro mai kama da siyasa.

Ziyarar ta El-Rufai ta fara yamutsa hazo a fagen siyasa wadda wasu ke ganin tana nuna ina ya dosa a zaɓen 2027 da ke tafe ne.

El-Rufai ɗaya ne daga cikin waɗanda suka tsaya kai da fata sai Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya mulki ƙasar nan.

KU KUMA KARANTA: Ministan Harkokin Wajen Turkiyya ya gana da Haniyeh, jagoran siyasa na Hamas, kan tsagaita wuta a Gaza

Sai dai wani abin mamaki El-Rufain bai samu sahalewar Majalisar Dattawan Najeriya domin zama minista a gwamnatin da ya ba da gagarumar gudunmawa wurin kafawa ba.

Yayin wannan taro, an ga Sanata Teslim Folarin, na jam’iyyar APC  daga Jihar Oyo, da Sanata Nazif Suleiman, wani jigo a jam’iyyar PDP daga Jihar Bauchi.

A makon da ya gabata dai El-Rufai ya shirya wani shan ruwa inda aka ga mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu da Kashim Ibrahim-Imam (wani jigo a jam’iyyar APC), Shehu Musa Gabam shugaban jam’iyyar SPD na ƙasa, da waɗansu manyan ’yan siyasa.

Mai taimakawa Malam Nasiru a bangaren kafafen sadarwa Muyiwa Adekeye ya ce wannan taro ne kawai na sada zumunta wanda kowa na iya shiryawa.

Ya ce “tsabagen siyasar da ke zuciyar mutane ne ya sa ake yi wa ziyarce-ziyarcen fassarar siyasa, amma wannan ba wani abu ba ne, zumunci ne kawai.”

Muyiwa Adekeye ya yi wannan martani ne ga waɗanda ke cewa El-Rufai na shirin tsayawa takara ne a karkashin jam’iyyar SPD a zaɓen 2027.

Waɗansu hotunan ganawar El-Rufai da jiga-jigan jam’iyyar SDP

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Al'ajabi

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Published

on

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon bene mai hawa biyu a Jihar Legas, ya rushe yayin da ake tsaka da mamakon ruwan sama wanda ya haddasa ambaliya a wasu sassan jihar.

Ginin ya rushe ne a lamba 12 da ke yankin Cameroun kusa da Ewenla a Mushin.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (LASEMA), ta bayyana cewar bayan isar jami’anta wajen da lamarin ya faru, ta gano wani sabon gini mai hawa biyu ya rushe.

An ceto mutum bakwai; mata uku da maza huɗu, tuni aka kai su asibiti domin duba lafiyarsu.

KU KUMA KARANTA: Wani bene mai hawa 4 ya rufta da mutane a Abuja

Ya zuwa yanzu dai hukumar, ta ce babu wanda ya mutu a dalilin rushewar ginin.

Babban sakataren LASEMA, Dokta Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya ce ana ci gaba da gudanar aikin ceto don tabbatar da babu wanda ya maƙale a baraguzai.

Continue Reading

Labarai

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Published

on

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Rahotanni sun bayyana cewar wani jami’in Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC), ya hallaka kansa har lahira a Abuja.

An tsinci gawar marigayin ne a gidansa da ke babban birnin tarayya.

Marigayin, wanda ba a bayyana sunansa ba, an ce ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka yi kwas na 5 a makarantar horas da masu yi wa ƙasa hidima ta hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa.

An ruwaito cewar yana da ƙwazo da himma a wajen gudanar da ayyukansa.

Wata majiya ta ce jami’in ya jima yana fama da baƙin ciki da matsalolin rayuwa kafin mutuwarsa.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya shaida wa manema labarai cewa hukumar za ta binciki musababbin da ya sanya ya kashe kansa, kuma hukumar za ta taimaka wa iyalansa.

Oyewale, ya ƙara da cewa hukumar za ta binciki wasu abubuwa da suka haɗa da matsalar taɓin hankali da kuma matsalolin iyali waɗanda ka iya sanya ma’aikacin kashe kansa.

KU KUMA KARANTA: Ana zargin wani jami’in kwastam ya kashe kansa a Abuja

Sai dai ya ce hukumar ba za ta fitar da wata sanarwa ko kuma bayyana sunan jami’in ba, har sai an kammala bincike.

Continue Reading

Labarai

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Published

on

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC), ta rufe shaguna kusan 100 a babbar kasuwar Ogbete ta Jihar Enugu, bisa zargin sayar da wasu abubuwan sha na jabu.

Daraktan NAFDAC, Martins Iluyomade a yankin Kudu maso Gabas, ya ce hukumar ta ɗauki matakin ne bayan wani samame da ta kai a ranar Litinin.

A yayin samamen jami’an hukumar NAFDAC, sun cafke wata babbar mota ɗauke da kayayyakin maye tare da cafke wasu ‘yan kasuwa huɗu da ake zargi da hannu wajen sayar da jabun abubuwan sha.

Iluyomade, wanda masanin haɗa magunguna ne, ya nanata cewa matakin ya zama dole domin kare masu amfani da ire-iren kayayyakin .

Ya ce waɗanda ake zargin a halin yanzu ana kan bincikensu kuma za su fuskanci tuhuma a gaban kotu bayan kammala binciken.

KU KUMA KARANTA: NAFDAC ta haramta amfani da maganin tari na yara na kamfanin J&J

Har wa yau, ya nanata ƙudurin NAFDAC na kawar da kayayyaki marasa inganci, da jabun abubuwan ci da sha, da gurɓatattun kayayyaki a kasuwa.

Ya ƙara da cewa, an gudanar da binciken ne tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro.

A gefe guda kuma, ya bayyana muhimmancin aikin hukumar na tabbatar da lafiyar al’umma.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like