Rikicin ƙabilanci tsakanin al’ummomi biyu a gabashin Chadi ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 42, a yankin ƙasar da ke yawan fama da rikice-rikice a kan gonaki, a cewar Ma’aikatar Tsaro.
Ma’aikatar ba ta faɗi waɗanda ke da hannu a rikicin ba ko kuma tsawon lokacin da aka ɗauka ana yi, amma ana yawan samun rikici a yankin tsakanin manoma da makiyaya ko wasu ƙungiyoyin, duk a kan filaye.
A cikin sanarwar da ta fitar, ma’aikatar ta ce an kama mutum 175 a wajen da aka yi faɗan, inda wasu masu ɗauke da makamai suka cinna wa wani babban yanki na ƙauyen Tileguey a gundumar Ouaddai wuta.
“An shawo kan lamarin amma ina ƙoƙarin sasanta ɓangarorin,” kamar yadda Ministan Tsaro Janar Mahamat Charfadine Margui ya shaida wa AFP.
KU KUMA KARANTA: Rikici ya raba yara miliyan 1.8 da muhallansu a yankin Sahel – Save The Children
Ministan ya je wajen da aka yi rikicin, inda ya jagoranci wata tawagar gwamnati da sojojin da za su “bayar da cikakkun bayanai” a kan lamarin.
Ana yawan samun rikice a gabashi da kudancin Chadi, inda mazauna yankin da dama ke ɗauke da malamai, sakamakon yadda manoma ke zargin makiyaya da barin dabbobinsu suna cinye musu kayan amfanin gona.