Shugaban Najeriya ya haramta wa jami’an gwamnatin tarayya tafiye-tafiye ƙasahen waje

0
158

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya haramta wa jami’an gwamnatin tarayyar ƙasar da suka haɗa da ministoci da shugabannin hukumomi tafiye-tafiye ƙasashen waje na wucin gadi.

A wasiƙar da fadar gwamnatin ƙasar ta aike wa Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume mai ɗauke da kwanan watan 12 ga watan Maris, Shugaba Tinubun ya umarce shi da ya sanar da ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya matakin.

Haramcin zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Afrilun 2024, kuma zai ɗauki tsawon wata uku yana aiki.

Wasiƙar ta bayyana cewa an ɗauki matakin ne don a rage kashe kuɗaɗen gwamnati.

Matakin Fadar Shugaban Ƙasar na zuwa ne mako uku bayan da Majalisar Zartarwa ta amince da amfani da Rahoton Steve Oronsaye na shekara 12 baya, wanda ya ba da shawarar a haɗe wasu hukumomin gwamnati don a rage kashe kuɗaɗe.

KU KUMA KARANTA: Ƴan majalisar wakilan Najeriya na so a dinga bai wa masu takaba hutun wata biyar

Me wasiƙar Shugaban Ƙasar ke cewa?

  1. Shugaban Ƙasa ya damu da irin tsadar da ke tattare da tafiye-tafiye da ma’aikatu da hukumomin gwamnati ke yi da kuma yadda ake ƙara bukatar mambobin majalisar ministoci da shugabannin hukumomi su mayar da hankali kan ayyukansu don gudanar da ayyuka masu inganci.
  2. Bisa la’akari da kalubalen tattalin arziki da ake fama da shi a halin yanzu da kuma bukatar gudanar da harkokin kasafin kudi, na rubuto ne domin in sanar da umurnin Shugaban Ƙasa na sanya dokar hana tafiye-tafiye na wucin gadi ga dukkan jami’an gwamnatin tarayya a dukkan matakai har na tsawon watanni uku daga 1 ga watan Afrilun 2024

Bugu da ƙari, Tinubu ya ambaci cewa duk wani balaguron da ake yi da kuɗin gwamnati, ana buƙatar jami’an gwamnati su sami amincewa daga Fadar Shugaban Ƙasa, aƙalla makonni kafin tafiyar, tare da tabbatar da cewa tafiyar ta zama ‘wajibi’.

Sannan a watan Janairun da ya wuce ma Shugaban Ƙasar ya sanar da rage yawan mutanen da za a dinga yin duk wasu tafiye-tafiyen Gwamnatin Tarayya a ciki da wajen ƙasar.

Hakan ya faru ne bayan kakkausar sukar da gwamnati ta sha bayan halartar taron Sauyin Yanayi da ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa a watan Disamban bara, inda aka tafi da babbar tawaga ta mutane da dama.

An yi ta kokawa kan yadda aka kashe kuɗaɗe a wannan tafiyar a daidai lokacin da ake fama da tsadar rayuwa a ƙasar da raɗaɗin cire tallafin fetur.

Leave a Reply