Rikici ya raba yara miliyan 1.8 da muhallansu a yankin Sahel – Save The Children

Rikice-rikice da ake fama da su a ƙasashen Mali da Burkina Faso da Nijar, sun tilasta wa yara kusan miliyan 1.8 barin gidajensu, wanda ke nuna ƙaruwar hakan sau biyar cikin shekaru biyar da suka gabata, in ji ƙungiyar agaji ta Save the Children a ranar Alhamis.

Ƙungiyar mai zaman kanta ta ƙididdige adadin yaran da suka rasa matsugunansu a kasashen Sahel uku ta hanyar yin nazari kan alkaluman hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNHCR) da gwamnatocin kasashe da kuma kungiyar kula da masu ƙaura ta duniya (IOM).

Binciken ya nuna cewa adadin yaran da aka tilasta wa barin gidajensu ya ƙaru daga kusan 321,000 a shekarar 2019 zuwa kusan miliyan 1.8 a yau.

“Rikicin, wanda aka manta da shi a tsakiyar Sahel ya kasance daya daga cikin mafi munin bala’in gaggawa na jinƙai a duniya, wanda ya fi muni la’akari da yadda cewa wannan rikicin ya fi shafar yara kuma mafi ƙarancin shekaru a duniya,” in ji Vishna Shah, Daraktar Ƙungiyar a yankin Sahel.

Ta ƙara da cewa, “Miliyoyin yara na rayuwa ne a cikin ƙaurace wa mummunan rikicin da ba za a iya misalta su ba, wadannan yaran sun riga sun kasance za su taso a daya daga cikin wuraren da ke da wahala a duniya sakamakon rasa gidajensu da al’ummominsu da duk abin da suka sani.”

KU KUMA KARANTA: Australia ta goyi bayan ƙudurin MƊD na tsagaita wuta a Gaza

Ita ma ƙasar Cote d’Ivoire wacce ta fice daga yakin basasar da ta yi a shekarar 2011, ƙamarin da tashe-tashen hankula a yankin Sahel ke yi na shafarta, in ji kungiyar Save the Children.

Rikici a makwabciyarta Burkina Faso da Mali ya haifar da karuwar yara masu neman mafaka sau goma sha biyu a kasar, daga kusan 2,450 a karshen shekarar 2022 zuwa kusan 29,700 a halin yanzu.

Yara su ne kashi 40 cikin 100 na mutanen da ke gudun hijira a duniya, a cewar Majalisar Dinkin Duniya, amma sun fi yawa a yammaci da tsakiyar Afirka.

Sun kai kusan kashi 58 cikin 100 na waɗanda aka tilasta musu yin gudun hijira, a cikin nazarin da Save the Children ta yi.

Ƙasashen Burkina Faso da Mali da Nijar dai na fama da tashe-tashen hankula da juyin mulki da fatara da ƙarancin abinci na tsawon shekaru.

Mummunan cin zarafi da ake yi wa yara a cikin rikice-rikice da suka hada da kisa da raunata su da sacewa da saka yara kanana cikin kungiyoyi masu dauke da makamai ko kuma a matsayin sojoji ya karu a cikin ‘yan shekarun nan, musamman a Mali, in ji kungiyar Save the Children.

Haka kuma yankin Sahel na kan gaba wajen fuskantar matsalar sauyin yanayi.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *