Blinken zai je Saudiyya da Masar domin tattaunawa kan tsagaita wuta a Gaza

0
126

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Anthony Blinken zai je Saudiyya da Masar a wannan makon domin tattaunawa kan yadda za a tsagaita wuta a rikicin da ake yi tsakanin Isra’ila da Gaza, da kuma yadda za a ƙara yawan kayan agajin da ake kaiwa Falasɗinu.

KU KUMA KARANTA: Sarkin Saudiyya ya yi ƙira kan kawo ƙarshen munanan laifukan da ake yi a Gaza

Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka Mattew Miller ne ya bayyana haka inda ya ce Blinken ɗin zai tattauna da jagororin Saudiyya a Jeddah a ranar Laraba inda a ranar Alhamis zai wuce birnin Alkahira na Masar domin tattaunawa da shugabannin Masar.

Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare a Gaza a kullum inda take kashe ɗumbin jama’a akasarinsu yara da mata.

Leave a Reply