Isra’ila ta yi ruwan bama-bamai a kan gidaje a Gaza, ta kashe Falasɗinawa 20 da ta yi wa ƙawanya

0
173

Jami’an kiwon lafiya na Gaza sun bayyana cewa da sanyin safiyar yau Talata ne aka kashe Falasɗinawa 20 a hare-haren da Isra’ila ta kai a Rafah da wasu yankuna a tsakiyar Gaza.

Jami’an kiwon lafiya na Gaza sun ce mutum 14 ne suka mutu kana wasu da dama suka jikkata, sakamakon hare-haren da Isra’ila ta kai kan gidaje da gidaje da dama a birnin Rafah da ke kudancin Gaza a kusa da kan iyakar Masar, inda Falasɗinawa sama da miliyan ɗaya suke samun mafaka,.

Wasu karin mutum shida sun mutu a wani harin da aka kai ta sama a wani gida a sansanin Al-Nuseirat da ke tsakiyar Gaza, in ji su.

A Deir al Balah, wani gari da ke tsakiyar Gaza mai tazarar kilomita 14 kudu da birnin Gaza, ƙarar fashe-fashe da suka haɗe da tsawa, da ruwan sama sun ƙara jefa iyalan da suka rasa matsugunansu a sansanonin cikin tashin hankali da fargaba.

KU KUMA KARANTA: Sama da yara 13,000 Isra’ila ta kashe a Gaza – UNICEF

“Ba za mu iya bambance tsakanin sautin tsawa da tashin bama-bamai ba,” in ji Shaban Abdel-Raouf, mahaifin ‘ya’ya biyar, ta wata manhajar tattaunawa.

“Mun kasance a da muna jiran damina muna roƙon Allah ya kawo ta da wuri. Amma a yau muna addu’ar kada a yi ruwa, mutanen da suka rasa matsugunansu suna cikin matuƙar wahala,” in ji shi.

Leave a Reply