Shugaban kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL), Mele Kyari, ya bayyana cewar matatar mai ta Fatakwal za ta koma bakin aiki a watan Afrilu mai zuwa.
Wata sanarwa ta ruwaito shugaban NNPCL, yana cewar an kammala ayyukan gyare-gyare a matatar wacce ta karɓi ganga dubu 450 ta ɗanyen mai ta hanyar tunkuɗowa daga jerin bututun da ke aiki.
Ya kuma ƙara da cewar, ana daf da kammala ayyukan gyare-gyare a matatun man Kaduna da Warri.
A cewar Mele Kyari, ana sa ran matatar man Kaduna ta fara aiki cikin watan Disamba me zuwa.
Hakan na zuwa ne bayan shekaru 3 da amincewa da kashe dala bilyan 1 da rabi wajen gyara matatar mai ta Fatakwal, ɗaya daga cikin mafi girma a Najeriya.
Matatar man Fatakwal ita ce mafi tsufa a Najeriya, wacce aka gina a 1965, shekaru 9 bayan da aka gano man fetur a ƙarƙashin fadamu da dazuzzukan yankin Delta, inda kogin Naija ya koma tekun Guinea.
KU KUMA KARANTA:Manyan hafsoshin tsaro da gwamnonin arewacin Najeriya sun gana kan satar mutane
An gina matatun man Warri da ke kusa da Fatakwal da na Kaduna da ke arewa maso tsakiyar Najeriya a shekarun da suka biyo baya, sannan aka ginawa matatar man Fatakwal sabon ɓangare a shekarar 1989.
Sai dai a ‘yan shekarun baya-bayan nan rashin aikin matatun yafi aikinsu yawa.
A wani labarin kuma, Majalisar Dattawan Najeriya ta yi watsi da rahoton zargin yin almundahana a aikin yiwa matatun man ƙasar garanbawul da NNPCL ya gudanar.
Duk da kazancewarta ƙasa mafi arziƙin man fetur a nahiyar Afirka, Najeriya ta dogara ne kacokan akan shigo da albarkatun man fetur daga ƙetare saboda gazawar nata matatun.