Isra’ila ta kashe tare da jikkata mutane da ‘dama’ da ke jiran agajin abinci a Gaza

0
99

Ma’aikatar Lafiya ta Falasɗinu a Gaza ta ce Isra’ila ta kai hari kan Falasdinawa da ke jiran agajin jinƙai a zirin Gaza da aka yi wa ƙawanya, lamarin da ya yi sanadiyar kashe tare da jikkata wasu da dama.

Ta kuma ƙara da cewa adadin waɗanda suka mutu na iya ƙaruwa yayin da aka kai gawarwaki akalla 21 da wasu fiye da 155 da suka jikkata zuwa asibitoci.

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar ta ce Falasɗinawa na jiran agajin jinƙai a mashigin Gaza na Kuwaiti, inda ta ce tana nuna shirin da Isra’ila ta yi na aiwatar da wani sabon kisan kiyashi mai ban tsoro.

Hukumar ta ce ana ci gaba da aikin kwashe wadanda suka mutu da waɗanda suka jikkata duk da ƙalubalen da yankin ke fuskanta.

Sanarwar ta ƙara da cewa adadin waɗanda suka mutu na iya ƙaruwa saboda mummunan yanayin da waɗanda suka jikkata ke ciki, waɗanda ake kula da su a asibitocin da ke kusa.

Kamfanin dillancin labaran ƙasar Falasɗinu WAFA ya tabbatar da cewa an kashe mutane da dama tare da jikkata wasu.

Sojojin Isra’ila kamar yadda suka saba sun nisantar da kansu daga sabon kisan gillar na Gaza, a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce sojojinta da suka mamaye yankin ba su yi luguden wuta kan Falasɗinawa da ke jiran agaji ba.

Mohammed Ghurab, daraktan bayar da agajin gaggawa a wani asibiti a arewacin Gaza, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP cewa, sojojin sun buɗe wuta kai-tsaye a kan mutanen da suka taru a zagayen dajin domin jiran wata motar abinci.

Wani ɗan jarida na AFP da ke wurin ya ga gawawwaki da kuma mutanen da aka harbe.

Leave a Reply