No menu items!

Sample Page Title

Date:

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarni a buɗe iyakokin ƙasar da na Nijar nan-take.

Mai magana da yawun Shugaban Ƙasar Ajuri Ngelele ne ya sanar da hakan a ranar Laraba, inda ya ce baya ga buɗe iyakokin, shugaban ya bayar da umarnin ɗage duka sauran takunkuman da Najeriyar ta saka wa Nijar.

Shugaban ya bayar da umarni kan a ɗage waɗannan takunkuman da aka saka wa Nijar nan take: –

1- Rufe iyakokin sama da ƙasa tsakanin Najeriya da Nijar da kuma hana zirga-zirgar jiragen sama na kasuwanci wanda ECOWAS ta saka.

2- Dakatar da duka cinikayya tsakanin Najeriya da Nijar, da dakatar da duka ayyukan da ke tsakanin Nijeriya da Nijar, daga ciki har da bai wa Nijar wutar lantarki.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Kano ta bayar da umarnin rufe duka gidaje gala a jihar

3- Riƙe ƙadarorin Nijar a bankunan ƙasashen ECOWAS da dakatar da kadarorin Nijar da ke a bankunan kasuwanci.

4- Dakatar da ba Nijar duk wani tallafi na kuɗi da daina cinikayya da duk wasu cibiyoyi musamman EBID da BOAD.

5- Haramcin tafiye-tafiye ga jami’an gwamnati da iyalansu

Haka kuma Shugaba Tinubu ya bayara da umarnin cire takunkumin tattalin arziƙi kan Jamhuriyar Guinea.

Wannan na zuwa ne bayan ECOWAS ta cire takunkuman da ta saka wa Nijar a kwanakin baya.

An shafe lokaci mai tsawo ana dambarwa tsakanin ECOWAS da Nijar da Burkina Faso da Mali, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce.

Dambarwar ta samo asali ne tun bayan da sojojin da ke mulkin Nijar suka yi wa Shugaba Mohamed Bazoum juyin mulki a 2023 wanda hakan ya ja ECOWAS ta saka wa Nijar ɗin takunkumi.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...