Firaiministan Haiti, Ariel Henry, ya yi murabus

0
101

Firaiministan Haiti, Ariel Henry, ya ajiye aikinsa a ranar Litinin sakamakon rikice-rikice da wani gawurtaccen gungun da ya shahara wurin tayar da tarzoma a ƙasar yake haifarwa, wanda har ya jawo aka soke babbar zaɓen ƙasar sau da dama.

“Mun amince da murabus dinsa bayan kafa kwamitin shugaban kasa na rikon kwarya tare da nada firaminista na wucin gadi,” in ji Irfaan Ali, wanda shi ne shugaban Guyana kuma shugaban ƙungiyar ƙasashen yankin Caribbean.

Shugabannin ƙasashe daga ƙasashen CARICOM 25 sun haɗu a Kingston da ke Jamaica domin tattaunawa ta musamman kan rikicin Haiti.

Bayan gudanar da tattaunawar, Henry mai shekara 74 wanda yake a Puerto Rico sakamakon lamura na tsaro tun daga 5 ga watan Maris, ya shaida wa CARICOM matakinsa na sauka.

KU KUMA KARANTA: Minista ya faɗi dalilin da ya sa ya yi murabus daga gwamnatin Tinubu

A ɗayan ɓangaren, gungun masu aikata laifukan na Haiti ya yi yunƙurin kai hari a ofisoshin ƴan sanda biyu da kuma Ma’aikatar Cikin Gida, sai dai ƴan sandan sun daƙile su, kamar yadda kafafen watsa labarai na ƙasar suka ruwaito.

Shugaban gungun Jimmy Cherizier wanda aka fi sani da “Barbecue,” harin da ya jagoranta ya jawo dubban fursunoni sun tsere daga gidajen yari.

A ranar 6 ga watan Maris ya yi gargaɗi kan cewa idan Firaiminista Henry bai sauka daga muƙaminsa ba, “ko dai Haiti ta zama aljanna ga baki ɗayanmu ko kuma ta zama wuta gare mu.”

Gungun masu aikata laifuka wanda ke son Henry ya sauka daga mulki, ya yi arangama da jami’an tsaro a ranar 2 da 3 ga watan Maris inda ya kai hari kan gidajen fursuna biyu a faɗin ƙasar.

Kusan fursunoni 4,000 suka tsere daga gidan yarin a lokacin arangamar inda aka kashe sama da mutum 12.

A ranar 4 ga watan Maris, gwamnatin ƙasar ta saka dokar ta-ɓaci domin kamo fursunonin da suka tsere inda ta saka dokar hana fita wadda ake aiwatarwa na wasu lokutan.

Gungun Cherizier ya yi yunƙurin ƙwace iko da babban filin jirgin babban birnin ƙasar sau da dama domin hana Henry komawa ƙasar.

Leave a Reply