‘Yan bindiga sun sace ‘yan makarantar Allo a Sakkwato

0
88

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun sace wasu ɗaliban makarantar allo ta almajirai a wani ƙauye da ake ƙira gidan Bakuso a jihar Sokkwato da ke Najeriya.

Wannan kuma na zuwa ne ranar da gwamnatin jihar ke ƙaddamar da yaye jami’an bayar da tsaro ga al’umma da ta horas.

Lamarin rashin tsaro a Najeriya na ci gaba da yin kwan gaba kwan baya, domin matakan da ake ɗauka sun ka sa hana ‘yan bindiga aika aikar su.

A jihar Sakkwato da ke arewa maso yammacin Najeriya, a daidai lokacin da gwamanatin jihar ke ƙaddamar da jami’an tsaron al’umma, ‘yan bindiga ne suka kutsa kai cikin wani gari da ake ƙira gidan Bakuso a ƙaramar hukumar Gada da ke gabashin jihar suka sace ɗalibai almajirai da adadin su bai ka sa goma sha biyar ba.

Liman Abubakar wanda shi ne malamin makarantar allon da aka sace almajiran, ya ce ‘yan bindigar sun shigo cikin tsakiyar gari sun kamo wata mata sai suka biyo ta wajen makarantarsa, inda almajiransa suka ji kukan wannan mata da suka kamo.

Ya ce ɗaliban nasa suna da yawa sai suka tashi su kai ta shiga cikin dakunansu yayin da ‘yan bindigar suka tisa ƙeyar wasu da dama daga cikin almajiran.

Ɗan majalisar jiha mai wakiltar yankin Kabiru Dauda ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma ya ce ana kan kokarin daukar matakan da suka dace don maganin wannan matsalar da makamantan ta a duk faɗin jihar.

KU KUMA KARANTA:Ɗalibi ɗaya ya kuɓuta daga cikin ‘yan makarantar da ‘yan bindiga suka sace a Kaduna

Duk a ranar daya ‘yan bindiga sun kai wani hari a kamarar hukumar Isa, inda suka kashe wasu mutane ciki har da hakimin ƙauyen.

Wakilin al’ummar a majalisar dokoki ta jiha, Habibu Halilu Moɗaci, ya ce ‘yan ta’addar suna cin karen su ba babbaka ne saboda jami’an da aka tura su fatattake su, ba su samu damar iya kawarda su ba.

Da yake gwamnatin Sokkwato ta bi sahun takwarorinta, kamar Katsina da Zamfara wajen samar da jami’an tsaron al’umma dan majalisar jihar ya ce akwai bukatar ayi da gaske.

A yayin haɗa wannan rahoto dai gwamnonin jihohin Kebbi, Zamfara, Katsina, Bauchi da tsohon mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan tsaro Janar Ali Gusau, mai ritaya suna a Sokoto, domin kaddamar da jami’an tsaron al’umma kuma daren washe garin ranar ne ‘yan bindiga suka yi wannan aika-aika.

Leave a Reply