Mata na fuskantar koma baya a fannonin rayuwa daban-daban – matan Najeriya

0
69

A yayın da ake bukin ranar mata ta duniya a ranar Juma’a 8 ga watan Maris na shekarar 2024, wanda aka yiwa taken Zuba jari ga mata: Haɓaka ci gaba, dubban mata na jan hankali a kan yiyuwar jefa Mata miliyan 340 a duniya cikin tsananin talauci idan ba a ɗauki matakan da suka dace cikin gaggawa ba.
A yanayin da ake ci a yanzu, duniya na fuskantar rikice-rikice da yawa, kama daga na yanki-yanki, ƙasa da ƙasa, zuwa ga matsalolin matsanancin talauci, yunwa, tsadar rayuwa, tashin farashin kayayyakin abinci masu alaƙa da matsin tattalin arziƙi da ƙaruwar tasirin sauyin yanayi.

Masu fafutukar neman an baiwa mata damammaki kamar takwarorinsu maza sun bayyana cewa za a iya magance waɗannan ƙalubalen ta hanyar matakan ƙarfafa mata, saka jari ga ci gaba mata, don su iya jagorantan sauyi cikin aminci da daidaito a duniya ga kowa.

KU KUMA KARANTA:Ministocin harkokin wajen Najeriya da Rasha sun tattauna kan zaman lafiyar yankin Sahel

Shin ina aka kwana a game da baiwa mata damammakin da suka dace kamar yadda ake fifita takwarorinsu maza, ƙwararriya a fannin sadarwa, Ambassada Khadija Ishaq Bawas, ta ce a wasu ƙasashen duniya da suka ci gaba Ana assasa wannan taken na shigar da mata a dama da su, sai dai a cikin gida wato Najeriya da sauran rina a kaba.

A nata ɓangaren, ‘yar siyasa kuma mai fafutukar ganin an shigar da mata fannin da saura muhimman fanonnin rayuwa, Onarable Zainab Buba Galadima ta bayyana cewa ganin alƙaluman da suka yi nuni da cewa idan ba a ɗauki matakan da suka dace cikin gaggawa ba mata miliyan 342 za su faɗa cikin tsananin talauci har yanzu ana rarrafe ba a kai ga ɗaukan mataki ba.

Sai dai ƙwararriya a fannin tattara haraji kuma ‘yar kasuwa malama Binta Gaude ta na mai ra’ayin cewa gaskiya mata sun sami ci gaba a fanonni da dama duk da cewa ba a kai ga inda ake so ba.

Alƙaluman ƙididdiga sun yi nuni da cewa da saura aiki a fannin ci gaban mata musamman ganin yadda akwai giɓi a fannin ba su damar su yi mulkin siyasa, jagoranci cibiyoyi ko kamfanoni masu zaman kansu lamarin da masu fafutuka suka ce abun a sake dubawa ne don ci gaba a duniya baki ɗaya.

Leave a Reply